- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya ce zai zama da ‘matukar ban mamaki’ ya halarci bikin rantsar Tinubu.
- Obi ya musanta shirin gudanar da zanga-zanga gabanin rantsar da zababben shugaban kasa mai jiran gado a yau 29 ga watan Mayu.
- Wannan martani na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin cewa tsohon gwamnan jihar Anambra da kungiyarsa ta Obident za su gudanar da zanga-zanga a dandalin Eagle Square.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya ce zai zama da ‘matukar ban mamaki’ ya halarci bikin rantsar da zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu,Punch ta rawaito.
Obi wanda ya yi magana ta bakin mai taimaka masa, Tai Obasi, ya kuma musanta shirin gudanar da zanga-zanga gabanin rantsar da zababben shugaban kasa mai jiran gado a yau.
KARANTA WANNAN: Turkashi: Gwamnan G5 Ya Mika Mulki,Ya Barwa Magajinsa Bashin Biliyan N187bn
Wannan martani na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin cewa tsohon gwamnan jihar Anambra da kungiyarsa ta Obident za su gudanar da zanga-zanga a kusa da dandalin Eagle Square domin yin rajistar nuna rashin jin dadinsu kan yadda gwamnatin tarayya ta dage kan rantsar da zababben shugaban kasa.
Obasi ya ce, “Ban san daga ina wannan rahoton ya fito ba. Ba mu san komai game da shi ba ko kuma su waye ke da hannu a wannan zanga-zangar da ake shirin yi.
“Amma zan iya gaya muku sarai cewa shugaban nawa bai san komai ba.
Shigowar kudin kasashen waje – Obi
“Shi Obi ne kuma mabiyansa Obident ne. Na yarda cewa a wasu lokuta, za su iya yi da kansu, ko ta yaya za ka gaya musu su kwantar da hankali.
“Wadannan mutanen sun fusata. Ba su ji daɗin yadda aka yi amfani da komai ba a kan Obi wanda ya ba su fata sosai. Suka bi shi suka yi ta jiransa.”
Da aka tambaye shi ko shugaban nasa zai halarci bikin rantsar da Tinubu ne biyo bayan rahotannin cewa jam’iyyun siyasa da ‘yan takararsu na shugaban kasa an aike musu da takardar gayyata da daidaikun mutane,
Mataimakawa Obi ya ce, “Shugabana mutum ne mai tawali’u kuma mai hankali wanda a koda yaushe yake neman zaman lafiya da hadin kan kasa baki daya.
“Sai dai zai yi matukar mamaki ya halarci zuwa bikin mutumin da yake kalubalantar nasararsa a gaban kotu.
“Shugaba na ba zai iya yin abin ban mamaki da rashin hankali ba. Ba zan iya tabbatar da ko ya sami gayyatar zuwa bikin rantsar da shi ba. Amma ina gaya muku ba za ku iya ganinsa a can ba.”
A wani labarin kuma, Tawagar Amurka Ta Isa Najeriya Don Halartar Bikin Rantsar da Tinubu
Tawagar kasar Amurka ta isa Najetiya domin halartar bikin rantsar da zababben shugaban kasa Bola Tinubu.
Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya,ne a ranar Lahadi 28 ga watan Mayu ya sanar da zuwansu gabanin bikin mika mulki.
Kasa da shugabannin kasashen duniya 65 ne ake sa ran za su halarci bikin rantsar da Tinubu.