Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, yace Hukumar Ƴan sanda a shirye take ta bayar da lasisin mallakar makami ga duk wani da zai yi amfani da shi wurin kare kanshi daga ƴan ta’adda.
Gwamna Masari ya sanar da hakan ne a lokacin da yake ganawa da Manema Labarai a yau talata.
Kamar yadda Gwamnan ya bayyana, Jami’an tsaro su kadai sunyi ƙaranci su yaki ƴan ta’adda, a sabili da haka sai jama’a sun tashi tsaye domin kare kansu daga hare -haren ƴan ta’adda.
KARANTA WANNAN LABARIN: Magidanci, Matar sa, Ɗan sa, sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Niger
Gwamnan daga nan sai yayi fatali da aikin ƴan sa kai, tare da nuna gamsuwa akan aikin ƴan Bijilanti.
Ya nuna bukatar da ke akwai na tallafawa ƴan Bijilanti da kayan aiki domin basu sukunin fatattakar yan ta’adda a yan kunan su.