Hukumar aikin hajji ta Najeriya NAHCON ta yi kira ga gwamnatin Saudiyya da ta sake duba batun dakatar da zirga-zirgar jiragen Najeriya kai tsaye zuwa kasar.
Alhaji Zikrullah Hassan shugaban hukumar NAHCON ne ya yi wannan kira a lokacin da ya ziyarci ofishin jakadancin Saudiyya da ke Najeriya a Abuja.
Solacebase ta bayar da rahoton cewa Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Saudiyya (GACA) a ranar 8 ga watan Disamba, ta sanar da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama daga Najeriya kai tsaye zuwa Saudi Arabiya saboda cutar COVID-19.
Hassan ya bayyana cewa sun kai ziyarar ne domin tattauna batutuwan da suka shafi kasashen biyu, musamman dangane da ziyarar da Musulman Najeriya ke yi a kasar Saudiyya duk shekara.
Shugaban ya kara da cewa sun kai ziyarar ne domin neman a dage dokar hana zirga-zirga kamar yadda gwamnatin tarayya ta bukata.
“Bukata ce da aka riga aka gabatar ta hannun Ma’aikatar Harkokin Waje da sauran hukumomin,” in ji shi.
Hassan ya yaba da irin goyon baya da hadin kai da Masarautar take baiwa hukumar NAHCON da ma Najeriya baki daya.
Ya kuma yabawa mahukuntan Saudiyya kan kokarin da suke yi na tabbatar da biyan diyya ga iyalan wadanda suka mutu a shekarar 2015 da wani katafaren ginin kurgin da ya ruguje a Makka.
Da yake mayar da martani, jakadan Saudiyya a Najeriya, Faisal Bin Ibraheem Al-Ghamidy, ya bayyana fatan cewa nan ba da dadewa ba za a kawo karshen dakatarwar.
Ya yi alkawarin ba kasarsa goyon baya ga Najeriya a duk lokacin da ya dace.
Dangane da diyyar kurgin, jami’in diflomasiyyar ya ce Saudiyya na kokarin ganin an biya diyya ga magada ko wakilan wadanda abun ya shafa cikin gaggawa.
(NAN)