A yau Alhamis, Hukumar da’ar Ma’aikata ta Tarayya (FCC) ta musanta rahotannin da ke cewa ta fara daukar sabbin ma’aikata.
Shugaban hukumar na kasa FCC, Dr Muheeba Dankaka, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a da sadarwa na hukumar, Dr Chuks Okoli, ya fitar ranar Alhamis a Abuja.
Dankaka ya musanta rahotannin da ke cewa ana ci gaba da daukar ma’aikata a hukumar, ta hanyar amfani da shafin sa na Facebook.
“Hukumar ta lura, cikin takaici, wani asusun Facebook na bogi da ake yadawa, wanda ake zargin na shugaban hukumar FCC, Dr Muheeba Dankaka ne.
“Masu gudanarwa asusun Facebook na bogin, sun yi iƙirarin cewa ana ci gaba da ɗaukar ma’aikata a FCC,” in ji shi.
Dankaka ya yi kira ga jama’a da su lura cewa ba shi da asusun Facebook kuma babu wani daukar ma’aikata da ake yi a hukumar a yanzu.
“Don Allah a ku kula, kuma ban da wata alaka da masu damfara,” in ji sanarwar.