By Abbas Yakubu yaura
Hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya (NCS), reshen yankin Apapa, a ranar Laraba ta bayyana cewa, rundunar ta tara jimillar kudaden shiga da suka kai Naira 89,097,888,609.00 a matsayin kudaden shiga na watan Nuwamba.
Shugaban Hukumar hana fasa kwauri Kwanturola Malanta Yusuf ne ya bayyana haka a wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a, mataimakin Sufeto Janar na hukumar Abubakar Usman a Legas.
A cewar Yusuf, adadin da aka samu shi ne mafi girma da ake tarawa duk wata a hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya (NCS).
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “Wannan aikin na zuwa ne bayan hukumar ta samar da Naira biliyan 86 a cikin watan Oktoba sakamakon ingantattun ayyukan hadin gwiwa tsakanin hukumomin, da inganta harkokin kasuwanci, da gaggauta warware takaddama da hana asara kudaden shiga,” in ji shi.
Yusuf, wanda ya bayyana tara Naira biliyan 89b a matsayin mafarin samar da ingantattun kayan aikin na rundunar, ya kuma ce za a ci gaba da dorewar lokaci na karuwar kudaden shiga.
Sannan yace yana gode wa Kwanturolan Janar na hukumar hana fasa kwauri, Kanal Hameed Ali (mai ritaya) bisa goyon bayansa, da jagoranci wajen tura kayan aikin sirri na wucin gadi da ingantattun kayan aiki wanda ya kara wa hukumar kwarin gwiwa.
“Wannan tarin kudin na naira 89,097,888,609 wani ci gaba ne amma muna da burin sama da haka.” Matakin mu na farko shi ne inganta matakin bin masu ruwa da tsaki, wanda aka tantance na abin yabawa ne.
Yusuf ya yi nuni da cewa, a yayin da suke gudanar da harkokin kasuwanci, da tattara kudaden shiga da kuma samar da saukin gudanar da kasuwanci, hankalinsu kuma zai karkata ne kan al’amuran da suka shafi tsaron kasa.
Ya kara da cewa hakan zai ci gaba da bayyana a tsarin gwajin dakon kaya da musayar bayanan sirri da sauran hukumomin su abokan aiki.