By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire JAMB ta kara wasu darusa da suka hada Nazarin Kwamfuta, Physical da kuma health Education a matsayin wani bangare na darussan na UTME.
Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin sanarwarta ta mako-mako da Daraktan Hulda da Jama’a, Dakta Fabian Benjamin ya fitar, kuma ya bayyana wa manema labarai a Abuja ranar Litinin.
Ya ce daliban da suke da shirin yin jarabawar UTME yanzu za su iya zaɓar Nazarin Kwamfuta ko Health Education da Physical a matsayin wani ɓangare na darussan UTME guda huɗu da ake buƙata, idan suna so ko kuma kamar yadda zaɓin shirin su ya faɗa.
Hukumar ta ce kara darussa biyun zuwa darussa 23 na UTME da ake da su za su fara ne daga atisayen UTME na wannan shekarar 2022.
A cewar hukumar, an dauki wannan matakin ne don inganta guraben aikin yi na daliban da ke wucewa zuwa manyan makarantu.
Tare da ƙari, yanzu akwai darussan UTME 25 da ‘yan takara za su rubutawa.
Sauran sun hada da Kimiyyar Noma, Larabci, Art, Biology, Chemistry, Nazarin Addinin Kirista, Kasuwanci, Tattalin Arziki, Faransanci, Geography, Government, Hausa, Tarihi, da Tattalin Arzikin Gida.
Sauran sun hada da Igbo, Islamic Studies, Literature in English, Mathematics, Music, Physics, Principles of Accounts, use of English, da kuma Yarbanci.