Hukumar kidaya ta karyata jita-jitar daukar ma’aikata
Hukumar kidaya ta kasa ta ƙaryata batun ɗaukar aiki, inda ta bayyana hakan a matsayin yaudara da karya, rahotannin da ke cewa tana daukar ma’aikata ne domin kidayar jama’a da gidaje.
Wata sanarwa da jami’in NPC ya fitar a shafin sa na X, ta ce wasu bata gari ne ke yada jita-jitar daukar ma’aikata a shafukan sada zumunta daban-daban.
KARANTA WANNAN LABARIN:Rashin Tsaro: Ku yi addu’ar zaman lafiya a Zamfara – Gwamna Lawal ga mazauna jihar
“Muna so mu bayyana ba shakka cewa Hukumar ba ta fitar da irin wannan sanarwar da ake yadawa a cikin wannan lokaci ba.
“Hukumar na son sanar da jama’a cewa ba a gudanar da wani aikin daukar ma’aikata don kidayar jama’a a halin yanzu kuma tuni ta kammala daukar ma’aikata don kidayar jama’a na gaba kafin a dage aikin.
“A duk lokacin da shugaban kasa ya tsayar da sabuwar ranar da za a gudanar da kidayar yawan jama’a da gidaje masu zuwa kuma idan akwai bukatar a sabunta jerin sunayen ‘yan takarar da aka zaba kafin gudanar da kidayar jama’a, za a sanar da shi a kafafen yada labarai na kasa da kafofin watsa labarai da gidan jaridu na yanar gizo.
Ya bukaci jama’a da su yi watsi da bayanan karya da ke yawo a yanar gizo, su guji fadawa hannun ‘yan damfara.
“An shawarci ‘yan Najeriya da su rika samun ingantattun bayanai game da ayyukan Hukumar a kan shafukan yanar gizo na PC da kuma shafukan intanet.
“Za mu ci gaba da sabunta jama’a game da abubuwan da suka faru game da yadda aka gudanar da ƙidayar yawan jama’a da gidaje na farko a Najeriya yayin da abubuwan ke faruwa. Muna kira ga kowa da kowa da ya goyi bayan Hukumar don tabbatar da nasarar aikin ƙidayar jama’a.
A wani labarin kuma:Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Lawan ya rasa mahaifiyar sa
Iyalan tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan sun sanar da rasuwar mahaifiyarsu Hajiya Halima (Baba) Ibrahim.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai baiwa Lawan shawara kan harkokin yada labarai Ezrel Tabiowo ya fitar ranar Asabar.