A jiya litinin Hukumar kidayar jama’a ta kasa rashen jihar kebbi ta kaddamar da bude shafinta don daukan ma’aikatan wucin gadi a hedkwatar hukumar dake Birnin Kebbi, dangane da kidayar jama’ar da zai gudana a shekarar 2023
Da yake jawabi a wajen taron, kwamishinan ma’aikatar kula da kidayar ta kasa Dakta. halliru Bala Jikan Daudu ya bayyana cewa, sun fitar da wannan tsari ne domin tabbatar da gudanar da dauka ma’aikatan bisa gaskiya da adalci. Ya na mai cigaba da cewa, Hukumar za ta tabbatar da yin adalci a dukkan kananan hukumomi 21 na jihar Kebbi.
A WANI LABARIN KUMA: Wani dan takarar majalisar tarayya a Enugu ya rasa ransa
Dakta Halliru ya kara da cewa a shekarar 2023 za a dauki kimanin mutane miliyan daya da dubu dari biyar aiki fadin a Najeriya domin gudanar da aikin.
Dimokuradiyya ta ruwiato cewa, A wannan Karni na 21 kuma zamanin da ake amma fani da fasahar zamani, Kwamishinan ya ce yanzu Hukumar ta bude shafinta na yanargizo don yin rajistan neman aikin kuma kowane dan Najeriya da ya cancanta yana da hakki, saboda haka, daukar ma’aikata zai zama ta hanyar fasahar zamani
Kazalika, ƙidayar yawan jama’a ta ƙasa na da ikon tattarawa, tantancewa da yada bayanan alƙaluman Al’ummar dake cikin kasar nan.
Taron ya samu halartar Kwamishinan hukumar kulaa da Kidayar jama’an na kasa, wakilan hukumar na reshen jihar Kebbi, da wakilan kafafen yada labarai dake nan na jihar Kebbi da kuma wasu daga Jaridun daban daban.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ganduje Ya Kawo Ƙarshen Rikicin Alhassan Doguwa Da Murtala Garo
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya kawo karshen rashin jituwar dake tsakanin Alhassan Ado Doguwa da Murtala Sule Garo.
Danbarwar da ta barke tsakanin bangarorin ya haifarwa da jam’iyyar APC mai mulki, rikicin cikin gida da ya nemi tarwatsa ta.