Hukumar kwallon ƙafar Ingila ta ƙara cirewa Everton maki karo na biyu a wannan kakar
Ƙungiyar kwallon kafa ta Everton da Nottingham Forest sun keta dokokin kashe kudade.
Premier League ta mika Everton ɗin da Nottingham Forest ga wani kwamiti mai zaman kansa ranar Litinin bayan amincewa da keta dokokin kudi.
Laifukan da ake zargin su shine keta dokar cinikayya da wasu ka’idojin wanda ya shafi kakar wasa ta 2022/23, kuma laifin na iya kaiwa ga cire ma ƙungiyoyin maki.
A halin yanzu Everton da Forest suna fafutukar ganin sun fice daga matsayin da zai kai su ga buga kofin gajiyayyu (relegation) wanda ka iya jefa burin su cikin shakku.
A kwanakin baya dai Hukumar ta cirewa Everton maki 10 a kakar wasa ta bana saboda wuce ƙa’idar cinikayya a kakar da ta gabata ta 2021/2022.
KARANTA WANNAN LABARIN:Wata Mummunar Gobara Ta Lakume Dukiya Ta Miliyoyin Naira A Jihar Kwara
Kulob din na Merseyside na daukaka kara kan wannan takunkumin wanda ke matsayin hukunci mafi girma a tarihin gasar Premier.
Everton da Nottingham Forest, kowannensu ya tabbatar wa da Premier League cewa sun saba wa ka’idojin riba da dorewar gasar (PSR) “in ji sanarwar Premier League.
Wannan ya faru ne sakamakon keta dokar sama da damar da aka ba da a lokacin kakar 2022/23.
A bisa ka’idar gasar Premier, a yanzu an mika kararrakin biyu ga shugaban kwamitin shari’a wanda zai nada kwamitoci daban-daban domin tantance hukuncin da ya dace ga ƙungiyoyin.
Kwamitocin sun kasance masu zaman kansu daga gasar Premier da kungiyoyin mambobi Ana sauraren shari’ar a cikin sirri tare da yanke hukuncin karshe na kwamitocin akan manhajar yanar gizon Premier League ”
Yanzu dai an mika dukkan shari’o’in biyu ga shugaban kwamitin shari’a mai zaman kansa wanda zai nada kwamitoci daban-daban domin tantance hukuncin da ya dace.
Everton ta lashi takobin “kare matsayinta” a cikin wata sanarwa da ta ce ” Premier League ba ta da ka’idojin da za su hana sanyawa kulob takunkumi kan zargin keta dokar kuɗaɗen da ake zarginta da aikatawa ba kamar sauran hukumomin gwamnati ba.