Hukumar Kwastam ta Nigeria shiyar Zone A ta ce, ta kama wata mota dauke da harsasai, wadanda aka boye a a cikin garin rogo a gari Igbo-Ora na Jihar Oyo.
Kwanturolan shiyyar, Hussein Kehinde Ejibun ne ya tabbatar da kamun hakan a jiya Litinin, ya ce an kama motar ne lokacin da jami’an Kwastam ke sintiri a yankin a daren ranar Lahadin data gabata.
Ejibunu ya ce direban da abokin aikinsan, sun yi watsi da motar lokacin da suka ga motar jami’an hukumar kwastam din.
“Abubuwan da aka gano sun hada da harsashi Bindiga guda 751 na kirar AAA, Lion Cartridges mai tsawon 70mm, buhunan garin rogo, da buhunan gumammiyar shinkafa.” Inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yar Sanda ta Bindige Yan’uwanta sabida ta handame wasu kudade
“An aje dukkannin kayayakin a Shelkwatar hukumar dake yankin don ci gaba da gudanar da bincike,” a cewar shi.
Ejibunu ya yi kira ga dukkannin al’umar kasar nan, da su dunga baiwa hukumar bayanai a lokacin da yadace, domin taimaka wa wajen yaki da fasa kwaurin makamai a kasar nan.