Hukumar kwastam ta Najeriya reshen jihar Ogun 1, ta yi watsi da wani faifan bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa An yada bidiyon ne da ke cewa an bude iyakar Idiroko domin gudanar da harkokin kasuwanci a matsayin yaudara.
Kwanturolan yankin Mista Bamidele Makinde ne ya bayyana haka ya yin da yake zantawa da manema labarai a Abeukuta ranar Talata.
KARANTA WANNAN Kwastom Za ta Tura Jorage Marasa Matuka Zuwa Wata Iyaka
Makinde ya bayyana cewa an sake bude iyakar Idiroko domin kasuwanci tun a shekarar 2022.
Kwanturolan yankin ya bayyana cewa “Iyakar Idiroko tare da wasu guda uku da ake sake budeaa a shekarar 2022 da umarnin gwamnatin da ta shude za ta ci gaba da kasancewa a bude don kasuwanci na halal“.
Sai dai Makinde ya yi gargadin cewa ” Duk wanda ya yi kasuwanci ta haramtacciyar hanya za a kama shi”.
Jaridar SOLACEBACE ta rawaito cewa Ya kuma bayyana cewa rundunar ta samu kimanin Naira miliyan 32.174 idan aka kwatanta da Naira 10,615,618,00 da aka karba a shekarar da ta gabata ta 2022.
A cewarsa, adadin ya nuna bambancin Naira 23,558,487,00 wanda hakan ya samu karin kusan kashi 69 cikin dari. (NAN)
A Wani Labarin Kuma ICPC Ta Gurfanar Da Wani Mutum A Gaban Kuliya
Hukumar ICPC, ta gurfanar da wani Umar Abubakar a gaban kuliya, bisa laifukan da suka shafi zunzurutun zamba.
Gurfanar da Abubakar ya biyo bayan yiwa wanda abin ya shafa alkawarin zai taimaka masa wajen samar masa da aiki tare da ICPC.