By Abbas Yakubu Yaura
Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa sun kama wasu masu safarar miyagun kwayoyi uku a kan iyaka a lokacin da suke kokarin safarar fakitin Tramadol guda 48,000 mai nauyin milgiram 225 mg ta hanyar Mubi da ke jihar Adamawa zuwa jamhuriyar Kamaru.
Hukumar ta NDLEA ta kuma ce an kama sama da kilogiram 1,500 na Loud da wasu haramtattun abubuwa da aka shigo da su a wasu hare-hare a jihohin Legas da Edo.
Daraktan yada labarai da bayar da shawarwari na hedikwatar NDLEA da ke Abuja, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
Babafemi, a cikin sanarwar, ya ce wadanda ake zargin, Mohammed Hussaini, mai shekaru 32; da kuma Adamu Bella mai shekaru 18 da Mohammed Umar mai shekaru 18 a mahadar Tsamiya, dake kan titin Madanya Mubi, na karamar hukumar Mubi ta Arewa a jihar Adamawa a ranar Juma’a, 28 ga watan Janairu, tare da boye kayayyakin a cikin fakitin wani magani.
Ya ce, “Lokacin da aka yi hira da su, sun yi ikirarin cewa za’a kai magungunan ne zuwa garin Bagira da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru don kai wa wasu ‘yan kasar Kamaru domin kai su Maroa a Kamaru.
“Hakan ya zo ne bayan wani samame makamancin haka a unguwar Alaba Rago dake Legas inda jami’an hukumar na jihar suka kama Loud guda 1,200 da aka shigo da su, wani nau’in tabar wiwi mai karfi da ake zargin an shigo da su jihar ne daga wata kasa mai makwabtaka da jihar dake jimlar nauyin kilogiram 1,229.
“A wani samame da aka kai ranar Laraba 26 ga watan Janairu a Suru Alaba, karamar hukumar Ajeromi-Ifelodun, Legas, jami’an tsaro sun kama wani Ibrahim Musa, dan shekaru 25, dauke da fakitin 18,530 na Tramadol, Rohynol, Diazepam, Exol-5, da kwalaben Codeine 138.
“A filin jirgin sama na Murtala Muhammed International Airport, MMIA, dake Ikeja Legas, jami’an SAHCO a harabar filin jirgin saman da suke fitar da kaya zuwa kasashen waje, a lokacin da suke aikin binciken kayan da suka saba yi, sun kama wani fasfo na kasashen duniya guda 22 na kasashe daban-daban guda 22 da aka boye a cikin buhun Gari da sauran kayan abinci.
“Tara daga cikin fasfo din uku ne kowannen su na Birtaniya da Faransa da Portugal, sauran su ne: na Najeriya guda 8; Ghana guda 4 dana kasar Kamaru guda 1. Hakazalika a filin jirgin, jami’an sun kwato fakiti 12 na tabar wiwi mai nauyin kilogiram 4.95 da aka boye a cikin kwalin Golden Morn da aka shirya don fitar da su ta cikin rumbun ajiyar kayayyaki na SAHCO.
“A jihar Filato, wata tawagar jami’an NDLEA a ranar Juma’a 28 ga watan Janairu, ta kama wasu mutane biyu da ake zargi; Emeka Ezenwa mai shekaru 37 da Julius Akingbe mai shekaru 45 da haihuwa, bisa laifin mallakar kwayar methamphetamine kilogiram 126.5 da aka boye a cikin na’urar DVD da ta fito daga Legas, yayin da wani samame a karamar hukumar Kampani Zera-Wase ta jihar a ranar Juma’a ya kai ga kama Fatima Sadiq mai shekaru 20, wanda aka kama da tabar wiwi kilo 21.3.”
Kakakin hukumar ta NDLEA, ya ce wani samame da aka kai a ranar Juma’a a wani katafaren kamfanin hada magunguna, Bakin Kogi Ringim, jihar Jigawa, ya kai ga gano nau’o’in tabar wiwi, da Diazepam, Exol-5 da wasu sabbin sinadarai masu nauyin kilogiram 8.680kg. haka kuma da makamai kamar su wukake, injin yankan katako, sandunan Gora, katafila da layoyi.
“A jihar Edo jami’an tsaro sun kwato buhu 19 na tabar wiwi mai nauyin kilogiram 144.10 da aka ajiye a daji a kan titin Uromi, karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas da ake shirin jigilarsu zuwa wasu sassan kasar nan, yayin da aka kwato buhunan tabar wiwi guda takwas masu nauyin kilogiram 111.a daji a Iruekpen, dake karamar hukumar Esan ta yamma.
“Shugaban Hukumar ta NDLEA, Brig. Janar Mohamed Buba Marwa (Mai Ritaya) ya yabawa jami’ai da mazan Legas, MMIA, Adamawa, Filato da Edo na hukumar bisa jajircewar su da kuma yin taka-tsantsan.sannan ya kuma gargade su tare da takwarorinsu na fadin kasar nan da kada su sassauta har sai an kwato kilogiram na karshe na miyagun kwayoyi daga kowane sashe na Nijeriya,” a cewar sa.