Daga: Abbas Yakubu Yaura
Hukumar raya yankin Arewa maso Gabas ta bayar da tallafin kayayyakin kiwon lafiya na miliyoyin naira ga cibiyoyin kiwon lafiya a jihar Borno da yaki ya daidaita domin tallafa wa wadanda rikicin ta’addanci ya shafa.
Hukumar NEDC ta kuma bayar da gudunmuwar Naira miliyan 480 ga Jami’ar Maiduguri domin tallafa wa ayyukan binciken cutar daji.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/gwamnan-ondo-akeredolu-ya-bada-umurnin-a-kori-dukkan-maaikatan-da-ke-karban-albashi-fiye-da-daya/
Babban Sakatare na Ma’aikatar Agaji, kula da Bala’oi, da Ci gaban Al’umma, Dokta Nasir Sani Gwarzo ne ya bayyana haka a lokacin da yake mika kayan aikin ga sashin kula da harkokin jin kai na rundunar Sojoji ta 7 da ke Maiduguri ranar Laraba.
Gwarzo ya ci gaba da cewa, duk da kalubalen da kasar ke fuskanta a halin yanzu, sojojin sun cancanci goyon bayan sadaukarwar da suke yi da kuma jajircewarsu, yana mai cewa NEDC za ta ci gaba da tallafa wa sojoji wajen dawo da zaman lafiya a yankin.
Ya bayyana cewa, hukumar ta bayar da gudummawa kayan aikin jinya ga cibiyoyin lafiya uku da jami’ar Maiduguri da suka hada da na’urar X-ray na Analogue mai dauke da digitizer da sauran su zuwa shiyya ta 7 ta asibitin sojojin Najeriya, kayan asibiti, da injin Janareta mai 500KVA ga Asibitin Neuropsychiatric na Gwamnatin Tarayya Maiduguri; gadaje na asibiti guda 200 da kayan aiki zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri.
“Zan so in mika muku wannan muhimmin kayan aiki, mun yi imani da wadannan karin rayuka za a sami cetowa. Kayan aiki sun haɗa da na’urar X-ray na Analogue tare da digitizer, na’urar sauti mai tsaka-tsaki tare da kayan bincike 3 da saitin janareta na 500K da kuma kayan aikin likita masu yawa.”
“Wannan aikin abin yabawa ne. Muna alfahari da NEDC don wannan kyakkyawan aikin da zai inganta ayyukan kiwon lafiya,” in ji Gwarzo.
A nasa jawabin, Manajan Daraktan Hukumar NEDC, Mohammed Alkali ya ce hukumar za ta tallafa wa al’ummar yankin da ayyukan da za su samar da dawwamammen zaman lafiya ga jama’a.
Da yake mayar da martani, babban kwamandan runduna ta 7 ta sojojin Najeriya, Manjo Janar W Shaibu ya godewa hukumar NEDC da tawagarta bisa tallafin da suke baiwa jamk’an sojojin da iyalansu.
Sannan ya ba da tabbacin cewa za a yi amfani da dukkan kayan aikin da aka yi niyya don amfanin Operation Hadin Kai.
“Ina son in jinjinawa hukumar NEDC bisa wannan kyakkyawan karimcin kuma ina amfani da wannan kafar don nuna jin dadinmu ga shugabanni kan wannan nuna kauna da kulawa ga sojojin Najeriya da jami’anta,” in ji Shaibu.
A nasa bangaren, Daraktan kula da lafiya na asibitin masu tabin hankali na gwamnatin tarayya dake Maiduguri Dr. Ibrahim Abdu Wakawa ya godewa hukumar tare da bayyana hakan a matsayin taimakon ceton rai ba ga asibitin ba, illa ga daukacin yankin Arewa maso Gabas.