By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar tsaro ta NSCDC reshen jihar Katsina ta kama wasu mutane uku da ake zargin manyan barayin wayar lantarki ne.
Daga cikin wadanda ake zargin suna da hannu wajen lalata manyan igiyoyin wutar lantarki da ke kan titin Sabongida zuwa Bugaje, a karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina, har da wani Haris Ishaq mai shekaru 58 da wasu mutane biyu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-dumi: 2023: Ku Bani Dama In Zabi Wanda Zai Gajeni – Buhari Ya Roki Gwamnonin APC
Kakakin rundunar, DSC Mohammed Abdara, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da wanda ake zargin yayin wani taron manema labarai a ranar Talata a Katsina.
Abdara ya ce, rundunar tsaro ta farin kaya da ke yaki da barnatar da kayayyakin jama’a da ke aikin sintiri na yau da kullum a yankin sun cafke wadanda ake zargin wadanda suka amsa laifin sayar da wasu igiyoyin da aka lalata.
“Wannan nasarar ta zo ne a sakamakon kudurin da muka dauka na yaki da duk wani nau’in laifuffuka a jihar.
Haris Ishaq wanda dan kauyen Yangero ne da ke karamar hukumar Jibia, ya bayyana cewa ya aikata laifin, in ji Abdara.
Ya bayyana sunayen wasu mutane biyu da aka kama tare da Haris mai suna Auwal Hamisu dan shekara 28, da Ibrahim Sabi mai shekaru 35.
Yayin da Sabi mazaunin Sabongida Quarters, ya taimaka wa wanda ake zargi da aikata laifin, Hamisu, mazaunin unguwar Yarnmawa a cikin birnin Katsina ya siyo kilo 30 na igiyoyin a kan kudi Naira 9500, Abdara ya bayyana.
A cewar kakakin hukumar NSCDC, an kammala bincike kan lamarin kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wanda ake zargin.
Abdara ya ce, rundunar NSCDC ta dukufa wajen hada kai da sauran hukumomin tsaro domin yakar miyagun laifuka da rashin tsaro a jihar, inda ya bukaci jama’a da su taimaka wa jami’an tsaro da ingantattun bayanan sirri domin ba su damar gudanar da aiki yadda ya kamata.