Hukumar Shige da Fice ta Damƙe masu Safarar Makamai 3 a Cross River
Kwanturolan da ke kula da Hukumar Shige da Fice ta Najeriya da ke Iyakar Mfum, kusa da Ikom a tsakiyar Jihar Kuros Riba, Mista Ndubuisi Eneregbu ya tabbatar da kama wasu mutane uku da ake zargin masu safarar makamai ne.
Ya tabbatar da hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a Calabar. Iyakar Mfum gari ne mai bunƙasa kasuwanci na ƙasa da ƙasa.
Eneregbu ya ce mutanen uku da ake zargin sun hada da ƴan Najeriya biyu da kuma wani dan kasar Kamaru ɗaya, waɗanda suka amsa cewa su ƴan kungiyar ƴan awaren Ambazonia ne.
Ya bayyana cewa an kama waɗanda ake zargin ne a kan babur ɗauke da makamai da kuma harsasai masu rai.
“An samu wadanda ake zargin dauke da wata karamar jaka dauke da muggan abubuwa kamar bindigar barrater daya, bindigar gida daya, alburusai masu rai guda uku, laya da wayar android TECNO BC3 guda daya.
“A cewar sa, su hudu ne kuma mutum na hudu a halin yanzu ya bar su da buhun da ke dauke da abubuwan da ba a taba gani ba.
“Bincike na farko ya nuna cewa daya daga cikin wadanda ake zargin dan kasar Kamaru dan kungiyar ƴan awaren Ambazonia ne a jamhuriyar Kamaru.
“An mika wadanda ake zargin guda uku tare da wadannan abubuwan ga jami’in ‘yan sanda na shiyya ta Etung da ke karamar hukumar Etung ta jihar domin ci gaba da bincike,” inji shi.