Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Alhaji Atiku Bagudu, ya ce za a samar da Naira biliyan 18 ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa domin tallafa musu wajen gudanar da zaben Bayelsa, Kogi da kuma Imo.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnatin jihar bayan kammala taron majalisar wanda shugaban kasa Bola Tinubu ya jagoranta a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa a Villa, Abuja.
Karanta nanZamu Sa Ido Akan Yadda Ake Amfanin Da Fasahar Zamani Ta AI A Nijeriya-Abbas
Hakanan an bayar da Naira biliyan 18 ga hukumar zabe mai zaman kanta don tallafa musu wajen gudanar da zaben Bayelsa, Kogi da Imo,” inji shi.
Hakazalika, ya kuma bayyana cewa, jimlar Naira tiriliyan 2.1, FEC ta amince da shi a matsayin karin kasafin kudi na shekarar 2023, wato na biyu a wannan shekarar.
Ya bayyana cewa, daga cikin kudin da ake shirin kashewa, za a kashe Naira biliyan 605 wajen samar da tsaro da tsaron kasa, yayin da za a kashe kimanin Naira biliyan 300 wajen gyaran gadoji.
Bagudu ya kuma bayyana cewa Naira biliyan 210 ne za a biya domin biyan albashin ma’aikatan gwamnati da kuma Naira biliyan 400 na kudaden da za a kai ga magidanta masu rauni.
A wani labarin kumaKu Fada Min Abinda Nayi Muku-Gwamna Fubara Ya Roki ‘Yan Majalisarsa
Ministan ya sanar da cewa an samar da Naira biliyan 100 a cikin kudirorin kasafin kudin a matsayin tallafin kayayyakin more rayuwa ga Babban Birnin Tarayya (FCT), da kuma wani Naira biliyan 800 ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) don gudanar da zaben Gwamna a Bayelsa. Jihohin Imo da Kogi.
An kuma saka wani tanadin Naira biliyan 8 a cikin karin kasafin kudin kaddamar da sabbin ma’aikatun da aka kirkiro kamar ma’aikatar ruwa da tattalin arziki ta Blue, a cewar Bagudu.