Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta yi wa shugaban kasa Bola Tinubu fatan samun nasara bayan nasarar da ya samu a kotun koli.
Sakataren NNPP na jihar Legas, Sheriff Oladejo ne ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a ranar Juma’a a Legas.
A cewarsa, nasarar da Tinubu ya samu a kotun koli zai ba shi damar mai da hankali sosai kan harkokin mulki ba kamar da da yake jiran hukuncin na kotu ba.
Karanta nanSokoto: Kotun Zabe Ta Yi Watsi da Kararrakin Da Aka Shigar Kan Wamakko Da Wasu
Mu a matsayinmu na jam’iyyar siyasa, ba mu je kotu ba saboda wasu dalilai da muka sani, amma wasu jam’iyyun siyasa na da cikakkiyar damar tuntubar kotu idan sun ga suna da korafi na gaske.
Yana da kyau a lura cewa dukkan bangarorin sun kai kokensu,kuma kotun karshe ta yanke hukunci.
Muna fatan daga wannan lokacin shugaban kasa zai maida hankali sosai kan aikin gudanar da mulki.
A matsayinmu na jam’iyya, muna yi wa shugaban kasa Bola Tinubu da jam’iyyarsa fatan sauka lafiya domin gudanar da harkokin jama’armu in ji Oladejo.
Kotun koli a ranar Alhamis ta amince da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa, wadda ta tabbatar da zaben Tinubu a ranar 25 ga watan Fabrairu.
A wani labarin kuma‘Babu Macen da Za ta Ce Bata Taba Zubar Da Cikin Sau Daya Ko Sau Biyu Ba’ – Phyna
Kotun ta yi watsi da karar da dan takarar jam’iyyar PDP a zaben Alhaji Atiku Abubakar da takwaransa na jam’iyyar Labour, Mista Peter Obi suka yi kan hukuncin da kotun ta yanke.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana nasarar da ya samu a kotun koli a matsayin nasara ga ‘yan Nijeriya baki daya domin zai janyo kowa a jikinsa domin ciyar da Nijeriya gaba.