Daga: Abbas Yakubu Yaura
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da sauran laifuka masu alaka da juna mai zaman kanta, ICPC, ta gurfanar da mataimakin kwamandan hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya (NSCDC), Mista Edike Mboutidem Akpan, bisa laifin damfarar wasu mamallaka gidaje Naira miliyan 26,655,000.
An gurfanar da Mista Akpan ne a gaban mai shari’a V. S. Gaba na babbar kotun birnin tarayya Abuja, da ke zamanta a Kwali, Abuja, kan tuhume-tuhume 17 da suka hada da amfani da wani kamfani mai zaman kansa, Danemy Nig Ltd, wajen damfarar masu mallakar filaye.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/rikicin-pdp-dalilin-da-ya-sa-gwamna-wike-ya-kusa-samun-bugun-zuciya-kola-ologbondiyan/
Takardar tuhumar ta nuna cewa mataimakin kwamandan ya shawo kan masu amfani da filaye da dama da ikirarin cewa suna hadaka da NSCDC, sun biya wasu makudan kudade na filayen da ke Karshi da Jihar Nasarawa da Sabon Lugbe Extension, titin filin jirgin sama, Abuja, wadanda ba a taba samu ba aka ware musu.
ICPC ta shaida wa kotun cewa laifin da aka aikata tsakanin shekarar 2010 zuwa 2015 ya saba wa sashe na 19 da 26 (1) (c) na dokar cin hanci da rashawa da sauran laifuffukan da ke da alaka da su ta 2000 kuma za’a hukunta shi a karkashin sashe na 19 na wannan dokar.
A daya daga cikin tuhume-tuhumen, Mista Akpan, ana zarginsa da yin amfani da abinda bai dace ba a kansa, inda ake zarginsa da karbar Naira miliyan 13,350,000 a shekarar 2011 daga hannun wani ma’aikaci mai suna Mista Igwe Onus Nwankwo, ta hanyar kamfaninsa Danemy Nig Ltd, a matsayin biyan kudin filaye guda 10 a Titin jigin sama.
A lokuta daban-daban ana zarginsa da karbar Naira miliyan 1,305,000 daga hannun wasu Likitoci da suka hadar da Robert Okoro da Akuneme Marcel Ikwuoma, kowannensu, domin rabon filayen da ake yi a tsarin gidajen da ake kira Defenders Family Estate Homes Scheme, da ke titin filin jirgin sama.
Ana kuma zargi jami’in NSCDC da karbar Naira miliyan 2,610,000 daga hannun Misis Chidinma Obasi kan wasu filayen guda biyu da kuma Naira miliyan 1,205,000 daga hannun Mista Etuechere Martins, kan wani fili.
Wanda ake zargin ya ce shi “Ba mai laifi bane” a lokacin da aka karanto masa kunshi tuhumar yayin da lauyansa ya roki kotu da ta bayar da belinsa bisa sharuddan sassauci.
Lauyan ICPC, John-Paul Okwor, wanda bai yi adawa da neman belin ba, ya roki kotu da ta amincewa wanda ake tuhumar a bayar da belinsa bisa sharuddan da suka dace da za su tabbatar da halartan shi a gaban kotu domin yi masa shari’a.
Daga nan ne mai shari’a Gaba ya amince da bayar da belinsa a kan kudi Naira miliyan 5 tare da mutane biyu da za su tsaya masa. Dole ne daya daga cikin wadanda za su tsaya masa ya nuna shaidar zama a gidansa na kashin kansa.
Kotun ta kuma ce dole ne wanda ake kara ya ajiye fasfo dinsa na kasa da kasa a gaban magatakardar kotun tare da bayar da sanarwar a ba shi idan ya nemi jinya. Daga nan aka daga shari’ar zuwa ranar 7 ga watan Nuwamba dan cigaba da shari’ar.
NAN