Idan har Emefiele ya Tsaya Takarar Shugaban Ƙasa, zan shigar dashi Ƙara 1000 — Gargaɗin Wani SAN
Ana cigaba da yin Allah wadai a ranar Talata sakamakon yunƙurin Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele na yin Takarar Shugaban Ƙasa a Shekarar 2023 a Jam’iyyar APC duk da yana kula da Babban Bankin Ƙasa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zanga Zangar Sri Lanka: Mutum 9 sun Mutu, Sama da 200 sun jikkata
Wani Babban Lauya Dr. Remi Olatubora (SAN) a ranar Talata yayi gargaɗin tattara ƴan Najeriya, da Ƙungiyoyin Al’umma domin su shigar da ƙara sama da 1000 akan Emefiele, idan har ya tsaya Takarar Shugaban Ƙasa a Shekarar 2023 a Jam’iyyar APC.
A cewar sa, zai tabbatar nan da Shekaru 10, Gwamnan Babban Bankin Najeriya zai riƙa tsallake daga wannan Kotu zuwa wannan sakamakon ɓata kuɗin ƙasa “lamarin da bai taɓa faruwa a tarihin Ɓangaren Shari’a a Najeriya.”
Emefiele a jawabin shi yace bai yanke hukuncin tsayawa Takara a Shekarar 2023.
A ranar Litinin Lauyan Emefiele Mike Ozekhome SAN ya shigar da ƙara mai lamba ta FHC/ABJ/CS/610/2022 yana ƙalubalantar halattar Sashe na 84(12) na sabuwar Dokar Zaɓe da aka gyara, domin hana dokar ta shafe shi, a ƙudirin shi na tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC.
Amma Olatubora, Tsohon Kwamishinan Ilmi a Jahar Ondo a lokacin Gwamnatin Dr. Olusegun Mimiko a tattauanawar sa Jaridar The PUNCH yace lauyoyin Emefiele su shirya domin suna da aiki mai yawa.
Comments 1