- Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa a shirye yake ya jagoranci tattauna da ‘yan bindiga domin Najeriya ta zaman lafiya
- Fitaccen malamin addinin musulincin ya bayyana cewa zai jagoranci shiga cikin lamarin idan har shugaba Bola Tinubu ya bukace shi da yin hakan.
- Sheikh Gumi ya ci gaba da cewa tattaunawa da ‘yan fashin dajin ba shi da alaƙa da shugabanci, sai dai yin amfani da hikima.
Shahararren malamin addinin musulunci Sheikh Ahmad Gumi ya bada sharuɗɗan tattaunawa da ‘yan bindiga.
Malamin mazaunin Kaduna a tattaunawarsa da Jaridar Daily Trust ya bayyana aniyar yin tattaunawa da ‘yan bindiga domin dawo da zaman lafiya a ƙasar nan.
Malamin addinin musulunci ya bayyana sharaɗin tattaunawa da yan fashin dajin
Sheikh Gumi ya ce zai shiga harkar idan har shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙace shi da ya yi hakan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu Ta Bayar Da Umarnin Kama Shugaban INEC?
Yayin da ya bayyana cewa ba lallai ne ya jagoranci tattaunawar ba, amma ya ce zai yi farin ciki ya kasancewa cikin duk wata kungiya da gwamnati ta aminta da ta jagoranci tattaunawar.
Ya kuma jaddada buƙatar samar da cikakken tsari wanda ya kunshi malamai, sarakuna da malaman jami’o’i da su haɗa kai domin ganin an dawo da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.
Ba lallai ne in jagoranta ba, amma zan ba da kai don shiga cikinsa. Ba batun shugabanci ba ne; samar da kyakkyawan tsari wanda ze magance batun.
Muna buƙatar sa hannun sarakuna da malamai da malaman jami’o’i da suka gudanar da bincike mai zurfi kan wadannan al’amura. Mu zauna tare domin a samu zaman lafiya, mu baiwa mutane damar komawa gonakinsu,” in ji Sheikh Gumi.
An Rage Mugun Iri, ‘Yan Sanda Sun Halaka ‘Yan Bindigan Da Suka Hana Mutane Sakewa
A WANI LABARIN KUMA: Rundunar ‘yan sanda a ranar Juma’a ta kama wasu gungun ‘yan bindiga da suka yi yunkurin aiwatar da wata dokar zaman gida ba bisa ka’ida ba a Enugu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Daniel Ndukwe ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Enugu da yammacin ranar
DSP Ndukwe ya bayyana cewa, a wata fita farauta da tawagar ‘yan sanda bayan wani artabu da ‘yan bindigar da suka yi da safiyar yau, ya kai ga gano gawarwakin ‘yan bindigar guda hudu a cikin dajin da ke Awkunanaw, a Enugu.