Kwamishinan yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Festus Okoye, ya ce an ba Sufeto Janar na ‘yan sanda, Alkali Baba umarnin ganawa da jam’iyyun siyasa da ‘yan takara.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa ganawar zasu yi ta ne domin, ganin yadda za a kaucewa samun tashin hankali, kafin, a lokacin, da kuma bayan zaben 2023.
KARANTA ANAN: Yan Wasan Kebbi United Sun Samu Layin Gayyata Daga Turai
Okoye ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Channels TV cikin wani shirin siyasa na su.
Da aka tambaye shi ko me hukumar ke yi na dakatar da kai hare-hare a cibiyoyinta, Okoye ya ce hukumomin tsaro za su samar da tsaro na hadin gwiwa ga duk wasu muhimman kadarorin tsaron kasa na INEC domin gudanar da zaben 2023.
Ya ce, “Farmaki na baya-bayan nan da muka samu wanda ya fito daga karamar hukumar Abeokuta. Kwana daya bayan haka, hukumar ta kira wani taron kwamitin tuntuba kan zabe da kuma taron na musamman, kuma mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro yana can, haka shima Sufeto Janar na ‘yan sanda na can.
“Shugabannin hukumomin tsaro daban-daban na can. Kuma wancan taro na musamman, an amince da cewa, hukumomin tsaro daban-daban za su samar da tsaro na hadin gwiwa ga dukkan muhimman kadarorin tsaron kasa na INEC da za su dace da gudanar da zaben 2023.” Inji Okoye.
A wani labarin kuma: ASUU Ta Bukaci Ministocin Ilimi Da Kwadago Su Gaggauta Murabus
Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) reshen Jami’ar Ilimi ta Tai Solarin (TASUED) da ke Ijagun a Jihar Ogun, ta bukaci Ministocin Ilimi da Kwadago, Adamu Adamu da Dokta Chris Ngige da su yi murabus.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Kungiyar ta bukaci su gaggauta sauka ne saboda iya gudanar da shugabancin da aka basu, wanda hakan ya sanya ilimin Manyan Makarantu a Najeriya ya shiga wani hali.
Comments 2