Jihar Kano za ta tabbatar da kulla alaka mai karfi na ilimi da Masar a matsayin hanyar karfafa alakar da ke tsakanin jihar da kasar ta Masar.
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ne ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar kasar Masar a masarautarsa.
A cewarsa, kasar Masar da jihar Kano, Tarihin ya nuna cewa, sun na da dadaddiyar alaka a tsakanin su.
Sarkin ya ce bangarorin biyu za su ci gajiyar kudurin karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ta fannin kuma ilimi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Matasa Sun Toshe Hanya, yayin da hadarin Mota ya kashe mutane 3 a Calabar
Tun da farko a nasa jawabin jakadan kasar Masar a Najeriya Ihab Mustapha ya ce, kasarsa za ta kara habaka alakar da ke tsakaninta da jihar Kano ta hanyar bude kofarta ga daliban jihar Kano, masu son yin karatu a jami’ar Al-Azhar domin samun ingantaccen ilimi.
Comments 1