Ina Da Tabbaci Tambuwal Zai Kawo Gagarumin Ci Gaba A Yankin Sa ~ Atiku Yabo
Wani Dan gwagwarmayar siyasa Alhaji Atiku Yabo ya taya tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Kuma Sanata Mai ci a halin yanzu Alhaji Aminu Waziri Tambuwal murnar Rantsar da shi da aka yi.
Alhaji Atiku Yabo ya bayyana tabbacin cewa, tsohon Gwamnan zai kawo gagarumin cigaba a yankin da yake wakilta dama Jihar Sokoto baki daya, musamman ta la’akari da dumbin ayyukan cigaba da ya shimfida a lokacin da yana Gwamna a Jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rikici Ya Kunno Kai a PDP, Mambobin Kwamitin Gudanarwa 7 Na Jam’iyyar Sunyi Murabus
Ya ce Majalisa ta goma, zata kasance daya daga cikin majalisun da suka yi fice, musamman yanda aka samu tsohon Gwamnan a cikin ta.
“Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya kasance jajirtacce ne, Mai dagewa, ga son talakawa, Kuma tabbas zai kawo cigaban da ba’a tsammani a yankin Daya ke wakilta, dama jihar Sokoto baki daya” Alhaji Atiku Yabo.
Sai yayi addu’a ga Allah daya yi jagoranci ga tsohon Gwamnan, ya bashi Ikon sauke nauyin da ke rataye a wuyan sa.
A wani labarin Kuma:
Duk motocin da rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta kwace daga hannun tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle, an mayar masa ne a ranar Asabar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Yazid Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar din da ta gabata ta wata tattaunawa ta wayar tarho, inda ya ce an mayar da motocin ne bisa bin umarnin babbar kotun tarayya da ke Gusau.