Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya ce yajin aikin da kungiyoyin kwadago ke shirin yi kan cin zarafin da aka yiwa Joe Ajaero, shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya ya dace.
Kungiyar kwadago ta NLC da kungiyar ‘yan Kasuwa ta Najeriya, TUC, sun shelanta yajin aikin a fadin kasar, domin nuna adawa da lamarin da ya faru a Owerri, babban birnin jihar Imo, a makon da ya gabata, inda wasu da ake zargin ‘yan bangar siyasa ne suka yi wa shugaban NLC dukan kawo wuka.
Karanta nanYanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Rattaba Hannu Kan Karin Kasafin Kudin N2.17tr
Da yake mayar da martani, Shehu Sani, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, ya goyi bayan matakin da kungiyar ta dauka, yana mai cewa yajin aikin zai aike da sako karara ga wadanda suka kai harin Ajaero.
Sani ya yi imanin cewa yajin aikin zai isar da sako karara ga wadanda suka kai harin Ajaero.
Sanarwar ta ce babu wata kungiyar kwadago da ke da alhakin da za ta nade hannunta ta ga ana cin zarafin shugabanninta ba tare da mayar da martani ba.
A wani labarin kumaGwamnatin Jahar Kaduna Za Ta Fara Mayar Da ‘Yan Gudun Hijira Garuruwansu
Wannan yajin aikin zai aike da sako karara ga masu son bin wannan hanya ta yin amfani da ‘yan barandan siyasa don tarwatsa zanga-zangar da musgunawa masu zanga-zangar ba abin yarda ba ne.
Masu shirya taron EndSARS na Abuja za su iya tunawa yadda aka kai musu hari a hedikwatar CBN yayin da suke nuna korafinsu akan abubuwan da ake yi musu na takurawa da muzgunawa.