Hamshakin Attajirin duniya, Bill gates ya ce har yanzu an kasa tattara gamsassun bayanan da za su fayyace dalilan da suka hana annobar korona ba ta tafka barnar halaka miliyoyin rayuka a nahiyar Afrika, kamar yadda hukumomin lafiya suka yi hasashe a watannin baya.
Bill Gates dake tsokacin cikin sakonsa na karshen shekara, ya bayyana farin ciki bisa kuskuren da ya yi a baya, na bayyana fargabar cewa annobar ta korona za ta halaka miliyoyin mutane a kasashe matalauta.
Bayan shafe shekara guda da barkewa, kawo yanzu adadin wadanda cutar ta kashe da kuma wadanda ke kamuwa da ita na kasa matuka, idan aka kwatanta da ta’adin da annobar ke yi a Amurka da nahiyar Turai.
Alkaluman lafiya na baya bayan nan sun nuna cewar, adadin mutanen da cutar Korona ke halakawa a Amurka, ya zarta barnar da take yi a Afrika ta Kudu da kashi 50.
A farkon shekarar 2020 ne dai hamshakin attajirin na duniya Bill gates ya yi gargadin cewa Afrika za ta iya zama nahiyar da annobar Korona za ta fi yiwa barna a duniya.