Tsohon ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, ya karyata rahotannin da ke cewa ya tsere kan zargin cin hanci da rashawa.
Biyo bayan dakatarwar shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, Abdulrasheed Bawa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a ranar Larabar da ta gabata, an samu rahotannin cewa Malami ya fice daga kasar ne da nufin kaucewa kama shi da bincike.
Malami wanda ya fito daga jihar Kebbi ya rike mukamin babban jami’in shari’a a kasar tsawon shekaru takwas na mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari. Lokacin da aka nada Bawa a matsayin shugaban EFCC a 2021, Malami ya shaida wa wannan majiyar jaridar nan musamman cewa ya ba shawarar bashi mukamin bisa cancantarsa.
KARANTA WANNAN LABARIN:Yo Ƙone Takardunsa Na Makaranta Har Da Shaidar Kammala Digiri Ɗinsa
“Na yi farin ciki da cewa yawancin maganganun da aka yi ba a kan iyawarsa, basirarsa aka yi ba. Ba a taɓa tambayar karfin ikonsa a duk faɗin ƙasar ”in ji shi a cikin Maris 2021.
Sai dai dakatarwar da aka yi wa Bawa a ranar Laraba ya tayar da kura game da makomar Malami.
Wata majiya a hukumar ta EFCC ta shaida wa wannan jarida cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa na da sha’awar jin ta bakin Malami hasarar sama da dalar Amurka biliyan 2.4 na kudaden shiga daga sayar da ganga miliyan 48 na danyen mai da aka yi ba bisa ka’ida ba a shekarar 2015 da ta hada da duk wani danyen mai da ake fitarwa zuwa kasashen waje da tallace-tallace ta Najeriya daga 2014 har zuwa yau.
Majiyar ta kara da cewa akwai sauran batutuwan da tsohon babban lauyan hukumar zai amsa idan a karshe ya amsa gayyatar.
Sai dai a wata hira ta musamman da aka yi da shi a daren jiya, Malami ya ce, “Ba’a gayyace ni daga hukumar EFCC ko wata hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ba. Ina nan a Najeriya kuma zan halarci daurin auren da za a yi da karfe 2:30 a Masallacin Sheikh Isiyaka Rabi’u, Kano.
“Ba ni da shirin barin Najeriya kuma zan yi farin ciki da girmama duk wata gayyata da wata hukuma za ta yi min. Ni dan Najeriya ne na gaskiya kuma na yi imani da aikin Najeriya.
“Zan bayar da kaina ga Najeriya da cibiyoyinta bisa bukata.”
A nasa bangaren, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, wanda shi ma hukumar EFCC ta gayyace shi, ya musanta zargin.
A wata hira da ya yi da shi ta wayar tarho, ya ce, “To, kila a tunaninsu suka gayyace ni, amma abin da na sani shi ne na je ganin tsohon shugaban (Bawa) a makon da ya gabata, kuma ban samu wata gayyata ba. Idan suna so su gayyace ni, ina nan.”
A wani labarin kuma:Gwamnan Kano Ya Yi Wasu Muhimman Nade-Nade
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada Sani Abdulkadir Dambo a matsayin shugaban hukumar tara haraji ta jihar Kano (KIRS).
Wanda aka nada babban manaja ne a sashen binciken haraji na hukumar tara haraji ta tarayya FIRS da ke Abuja.