Shahararriyar jarumar nan Ifeoluwa Otedola wacce aka fi sani da DJ Cuppy ta ce ba ta shirya zama uwa ba a yanzu.
A cikin wani hoto, ta bayyana soyayyarta ga yara amma ta ce ba ta shirya haihuwa ba tukuna.
KU KARANTA: NEMA Ta Karbi Yan Najeriya 148 Daga Jamhuriyyar Nijar
Ta ce: “Ina son yara amma ban shirya daukar ciki ba,” kamar yadda ta bayyana a cikin hoton Wanda take tare da yaro.
DJ Cuppy ta bayyana hakan ne a matsayin mayar da martani ga wani masoyinta Wanda ya ke mata shaguben cewa tana dauke da ciki.
Ta Kuma tabbatarwa da sauran masoyan ta cewa Bata shirya daukar juna biyu ba, Amma tana shaawar Yara.
A wani labarin Kuma: EFCC Ta Kama Tsohon Minista Kan Badakalar Aikin Wutar Mambila
Hukumar Yaki da masu yiwa Yiwa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) ta kama tsohon Ministan wutar lantarki, Sale Mamman.
Justice Watch ta rawaito cewa wata Majiya mai tushe ta bayyana cewa ana tsare da tsohon ministan a hedikwatar hukumar bayan kama shi da sanyin safiyar Laraba.