Indiya ta mika wa Brazil shugabancin G20
Indiya ta mika wa Brazil shugabancin G20 a hukumance a bikin rufe taron shekara-shekara da aka yi a New Delhi a karshen mako.
Firayim Ministan Indiya Narendra Modi ya kammala mika mulki ne ta hanyar mika ragamar shugabancin ga shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva.
KARANTA WANNAN LABARIN:Shari’a: Ɓata Lokacin Ku Kawai Kuke Yi, Ba Abinda Zai Canja A Kotun Gaba – Clarke ga Obi, Atiku
Indiya ce ke shugabancin G20 tun ranar 1 ga watan Disamba, lokacin da ta karbi ragamar mulki daga Indonesia, kuma za ta ci gaba da rike mukamin har zuwa ranar 30 ga Nuwamba.
A yayin taron na kwanaki biyu, kungiyar ta amince da sanarwar bai daya, wadda ta dauki alkawura kan batutuwa da dama, da suka hada da samar da abinci da makamashi, da sauyin yanayi, da kuma rangwamen bashi a duniya.
A wani labarin kuma:Cikin Bidiyo: Nijar Ta Fara Girke Sojoji A Iyakar Ta Da Benin
Wani faifan bidiyo ya bayyana da ke nuni da cewa ‘yan juyin mulkin jamhuriyar Nijar sun fara jibge sojoji a kan iyakar ƙasar da makwabciyarta, Benin, a dai dai lokacin da kungiyar ECOWAS ke shirin shiga tsakani na soji.
Wani kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan.