INEC ce kadai alhakin bayyana yadda za a iya tattara sakamakon Zaɓe – Kotu
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ce hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ce kadai ke da ikon tantance tsarin tattara sakamakon zabe da kuma mika shi.
Mai shari’a Emeka Nwite ya kuma bayyana cewa INEC ce kadai ke da hurumin bayar da umarnin yadda jami’in zabe zai mika sakamakon zaben da suka hada da adadin wadanda aka tantance da kuma sakamakon zaben.
KARANTA WANNAN LABARIN:Kano: Limaman Juma’a Sun Yí Huduba Kan Muhimmancin Zaben Gawuna
Mai shari’a Nwite ya ci gaba da cewa tattara sakamakon zabe da hannu a zabukan 2023 ba za a iya cewa ya saba wa tanadin dokar zabe ta 2022 ba.
Hukuncin ya kasance ne a kan karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1454/2022 da jam’iyyar Labour (LP) ta shigar, inda INEC ita ce wacce ake kara.
LP ta roki kotu da ta bayyana cewa INEC ba ta da ikon zabar hanyar da za’a tattara zaɓe ba, in ba hanyar intanet ba kamar yadda dokar zabe ta 2022 ta tanada.
Ta bukaci kotun da ta bayar da umarnin tilasta wa INEC bin dokar zabe, 2022 kan ƙin watsa sakamakon zabe ta hanyar yanar gizo.
A hukuncin da ya yanke a ranar 23 ga watan Junairu, 2023, Nwite ya ce wanda ya shigar da karar ya yi kuskuren fahimtar abin da dokar ta tanada, ya kuma yi watsi da karar.
A wani labarin kuma:Tinubu zai mulki Najeriya har 2031, sannan ya mika wa Ɗan Arewa – Joe Igbokwe
Mai baiwa gwamnan jihar Legas shawara na musamman kan magudanar ruwa, Joe Igbokwe ya bayyana cewa zababben shugaban kasa Bola Tinubu zai ci gaba da zama shugaban kasar Najeriya har zuwa shekarar 2031 sannan kuma ya mika mulki ga dan arewa wanda zai mulki kasar har zuwa 2039.
Igbokwe, wanda jigo ne a jam’iyyar APC mai mulki, ya bayyana haka a lokacin da yake mayar da martani ga wani sharhi da ya wallafa a shafinsa na Facebook.