INEC ta bayyana damuwa kan rashin tsaro gabanin zaben Kogi, Imo da Bayelsa
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana damuwarta dangane da karuwar matsalar rashin tsaro da ake fama da ita, gabanin zaben gwamnoni da za a gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba a jihohin Imo, Bayelsa, da Kogi.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, Sam Olumekun ya fitar, ya bukaci jam’iyyun siyasa da ‘yan takararsu da su kaucewa ayyuka da kalaman da za su iya zafafa harkokin siyasa.
KARANTA WANNAN LABARIN:Nan Bada Jimawa Za’a Dawo Da Baku Mai – Kwastam Ga Al’ummomin Kan Iyaka
“Hukumar ta damu da yawaitar rashin tsaro da tashe-tashen hankula da suka hada da fada tsakanin magoya bayan jam’iyyun siyasa da ‘yan takara a zabe mai zuwa,” inji shi.
Hukumar ta yi kira ga daukacin jam’iyyun siyasa da ‘yan takara da su guji furta kalamai da abubuwan da ka iya zafafa al’amuran siyasa, inda ta kara da cewa za ta ci gaba da sanya ido sosai kan lamarin tare da ci gaba da kulla huldar ta da hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali a jihohin uku.
A wani labarin kuma:Wata Sabuwa: Gwamnatin Tinubu Ta Shirya Tsaf Don Yashe Manyan Kogunan Najeriya
Ministan albarkatun ruwa da tsaftar mahalli, Farfesa Joseph Utsev, ya bayyana a karshen mako cewa ana shirin dawo da yashe kogunan Neja da Benue.
Ya ce aikin zai sauya dukkan hanyoyin tattalin arzikin jihohin Neja da Benue da kuma yaki da ambaliyar ruwa a yankin.