Ya zuwa yanzu dai hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa INEC ta tura sakamakon zabe 66,634 na zaben gwamnoni da na majalisun jihohi a dandalinta na IReV.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa jam’iyyun adawa da wasu ‘yan Najeriya sun caccaki INEC kan gazawarta na sanya sakamakon nan take a dandalinta na kallon sakamakon zabe IReV da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Kaiwa Jami’an EFCC Hari a Kaduna
Sai dai kuma hukumar ta bayyana cewa, tabarbarewar fasahohin da aka samu ya haifar da yada sakamako wanda da yawan masu suka suka ki amincewa.
Sai dai kuma kwanaki kadan ya rage a gudanar da zaben ranar 18 ga watan Maris, INEC ta ce an gyara batutuwan fasaha tare da tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za a mika sakamakon zaben nan take a dandalin na IReV.
Binciken da wakilinmu ya yi a ranar Asabar da karfe 9 na dare ya nuna cewa an saka sakamakon zabe a jihohi 28. Wanda Suka hada da jihar Ogun, an gabatar da sakamako 3,631; Filato, 2,552; Zamfara, 782; Yobe, 1,231; Taraba, 973; Sokoto, 1,017; Rivers, 4,042; Oyo; 4,537.
Sauran sun hada da Neja, 1,810; Nasarawa, 1,986; Legas, 7,014; Kwara, 1,687; Kebbi, 753; Katsina 2,285; Kano, 3,452; Kaduna, 4,537; Jigawa, 1,900; Gombe, 1,124; Enugu, 3,172; Ebonyi, 1,814; Delta, 2,556; Cross River, 1,477; Borno, 1,956; Benue, 2,481; Bauchi, 1,835; Akwa Ibom, 2,414; Adamawa, 1,871; da Abia, 1,745.
A wani labarin kuma, INEC Ta Dage Zaben Gwamna Dana ‘Yan Majalisu a Filato
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta dage zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokoki da za a yi ranar Asabar a garin Butura da ke karamar hukumar Bokkos a jihar Filato zuwa ranar Lahadi, sakamakon matsalar kayan aiki.
Kwamishinan zabe na jihar, Dakta Oliver Agundu, ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a Jos ranar Asabar.