INEC tace ta yiwa Sabbin Mutane sama da Miliyan 10 Katin Zaɓe
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta INEC tace sabbin mutanen da ta yiwa rajistar Katin Zaɓe yanzu yawan su yakai mutum Miliyan 10,487,972 ya zuwa 7 na safiyar ranar Litinin 27 ga watan Yuni.
Hukumar ta bayyana haka a cikin wata sanarwa data fitar na mako-mako a Abuja a ranar Litinin, ta bayyana cewar mutane miliyan 8,631,696 tuni sun kammala rajistar Katin Zaɓen su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mai Martaba Sarkin Kano Ya Dawo Daga Morocco
Ta kuma bayyana cewa mutane miliyan 3,250,449 sun kammala rajistar su a yanar gizo, a yayinda mutane miliyan 5,381,247 suka yi Rajistar su kai tsaye.
Jadawalin wadanda suka kammala rajistar ya nuna cewa Maza Miliyan 4,292,690 suka kammala rajisatar su, a yayinda kimanin mutane 4,339,006, haka zalika a rajistar ya nuna matasa miliyan 6,081,456 suka yi Rajistar da masu bukata ta musamman mutum 67,171.
Sanarwar ta nuna cewa INEC ta karɓi kimanin bukatar rajista guda 23,560,043 ciki harda waɗanda suke neman a canja masu wajen zabe, da kuma canja masu katin zaɓe, da bayanai.
Jadawalin ya kuma ƙara nuna cewa maza 12,317,963 suka tura buƙatar haka, sai mata 11,242,080, da masu buƙata ta musamman guda 187,904