Sama da mutane 80 ne suka mutu tare da jikkatar wasu daruruwa a kasar Yemen da yaki ya daidaita a ranar Alhamis bayan wani rabon kayan agaji da ya haifar da turmutsitsi mafi muni cikin shekaru goma, in ji jami’an Huthi.
Wani bala’i na baya-bayan nan da ya afku a kasar mafi talauci a yankin Larabawa ya zo ne kwanaki gabanin bukukuwan sallar Idin karama da musulmi suke yi a karshen watan azumin Ramadan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sallah: Gwamnatin Kano Ta Gwangwaje Yara Daurarru da Kayan Sawa A Wasu Gidajen Yarin Jihar
Akalla mutane “85 ne suka mutu sannan fiye da 322 suka jikkata” bayan turmutsitsin da aka yi a gundumar Bab al-Yemen da ke babban birnin kasar, in ji wani jami’in tsaron Huthi.
“Mata da yara na cikin wadanda suka mutu,” kamar yadda ya shaida wa AFP bisa sharadin boye sunansa saboda ba shi da izinin yin magana da ‘yan jarida.
Wani jami’in lafiya na biyu ya tabbatar da adadin mutanen.
Wakilin AFP a Sanaa da ke karkashin ikon Huthi ya ce lamarin ya faru ne a cikin wata makaranta da ake raba kayan agaji.
Daruruwan mutane ne suka taru domin karbar kayan agajin a hannu, a cewar shaidu.
An kai wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata zuwa asibitocin da ke kusa, kuma an kai wadanda ke da alhakin rarraba kayayyakin zuwa gidan yari, in ji ma’aikatar harkokin cikin gida a cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labaran Saba na ‘yan tawayen ya fitar.
Ma’aikatar ba ta bayar da takamaiman adadin mutane ba amma ta ce “mutane da dama ne suka mutu sakamakon turmutsitsin da aka yi a lokacin rabon kudaden da wasu ‘yan kasuwa suka yi ba kakkautawa”.
Shugaban siyasa na ‘yan tawayen Huthi Mahdi al-Mashat ya ce an kafa kwamitin da zai gudanar da bincike.
Wani jami’in tsaron Huthi ya ce an tsare mutane uku bisa zargin su da hannu a cikin lamarin.AFP
A wani labarin kuma, ‘Yan Sanda Na Gudanar Da Binciken Hallaka Wani Jami’i Da Soja Ya Yi
Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta ce tana gudanar da bincike a kan wani soja da ya bindige wani jami’in dan sanda mai suna Sajan Ahmed Ali, wanda ya kama motarsa dauke da wani abu da ake kyautata zaton tabar wiwi ne.
Lamarin ya faru ne a wani shingen binciken ababan hawa da ke Benishek, karamar hukumar Kaga a jihar a ranar Litinin, yayin da sojojin da ke cikin wata mota kirar Acura Sport Utility Vehicle, da wani Sajan U Yusufu ke tukawa.
Comments 1