- Hukumar kwallon kafa ta Italiya (FIGC) ta sanar a ranar Juma’a cewa ta nada Luciano Spalletti, a matsayin kocin zakarun Turai na Italiya
- Spalletti ya maye gurbin Roberto Mancini, wanda ya yi murabus ba zato ba tsammani
- Sha’awarsa da ƙwarewarsa za su kasance masu mahimmanci ga ƙalubalen da ke jiran Italiya a cikin watanni masu zuwa
Hukumar kwallon kafa ta Italiya (FIGC) ta sanar a ranar Juma’a cewa Luciano Spalletti, wanda ya jagoranci Napoli ta lashe gasar Seria A a bara, an nada shi a matsayin kocin zakarun Turai na Italiya.
Spalletti ya maye gurbin Roberto Mancini, wanda ya yi murabus ba zato ba tsammani a ranar Lahadin da ta gabata bayan shafe shekaru biyar yana aiki.
KARANTA WANNAN: EPL: Lokaci Ne Na Bakin Ciki – Pochettino Ya Magantu Kan Babban Raunin da Chelsea Ta Samu
Spalletti ya kawo karshen shekaru 33 da Napoli ta yi na jiran kofin Seria A bara kafin ya bar mukaminsa.
Hukumar ta FIGC ta ce a cikin wata sanarwa da ta fitar “Sun cimma yarjejeniya da Luciano Spalletti kan matsayin kocin tawagar ‘yan wasan Italiya daga ranar 1 ga watan Satumba”.
“Mu yi maraba da Spalletti,” in ji shugaban FIGC Gabriele Gravina, “Kungiyar ta kasa ta bukaci babban koci kuma ina matukar farin ciki da ya amince da jagorar fasaha na Azzurri.
“Sha’awarsa da ƙwarewarsa za su kasance masu mahimmanci ga ƙalubalen da ke jiran Italiya a cikin watanni masu zuwa.”
Bayanin da Spalletti zai gabatar a hukumance zai gudana ne a cibiyar horo ta kasa da ke Coverciano, kusa da Florence, kafin wasan neman cancantar shiga gasar Euro 2024 da Arewacin Macedonia da Ukraine, in ji FIGC.
Tuscan mai shekaru 64, shi ne zai jagoranci farfado da tawagar kwallon kafar kasar, wadda duk da lashe kofin Turai a shekarar 2021, ta kasa samun gurbin shiga gasar cin kofin duniya da aka yi a Qatar a shekarar 2022.
Italiya za ta je Arewacin Macedonia a ranar 9 ga watan Satumba kuma za ta karbi bakuncin Ukraine a Milan bayan kwanaki uku.
Italiya ce ta uku a rukunin C da maki uku bayan ta doke Malta da ci 2-0 da kuma rashin nasara a hannun Ingila da ci 2-1, wacce ke kan gaba da maki 12 a wasanni hudu.
Mancini, wanda ke jagorancin tun a watan Mayun shekarar 2018, ya yi murabus saboda “yanke shawara” kuma an zarge shi da rike mukamin kocin Saudiyya.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Mawaki Wizkid Ya Yi Babban Rashi
Mawakin Najeriya Ayodeji Balogun wanda aka fi sani da Wizkid ya rasa mahaifiyarsa.
Mahaifiyar Wizkid, Misis Jane Dolapo Balogun, ta rasu da misalin karfe 1:30 na safiyar ranar Juma’a.