Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya bayar da gudunmowar gida na Naira miliyan bakwai ga iyalan marigayi Mohammed Ali da wata mota ta murkushe a Damaturu a watan Agustan da ya gabata.
Da yake mika tallafin kudi da takardun gidan ga yaran a madadin Gwamna Buni, ta hannun mai martaba Sarkin Damaturu, Alhaji Shehu Hashimi II, Ibn Umar Al-Amin El-Kanemi, mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin addini Ustaz. Baba Gana Kyari ya jajanta wa ‘yan uwa tare da addu’ar Allah ya jikan marigayin.
Karanta nanKo Sau 100 Za A Sake Zabe A Jahar Zamfara Sai Na Lashe-Gwamna Dauda
Kyari ya bukaci matar da mijin na ta ya mutu da ta jajirce, inda ya ce ba a bayar da kudaden da sauran tallafin ne a matsayin fansa ba sai dai don rage musu wahalhalun da suke ciki, musamman sakamakon cire tallafin man fetur a Najeriya.
Gwamna Buni ya kuma yi alkawarin daukar nauyin karatun ‘ya’yan marigayi Isa da kuma ciyar da matarsa mai ciki.
A nasa jawabin bayan mika tallafin ga yaran, Sarkin Damaturu, Alhaji Dr. Shehu Hashimi na biyu Ibn Umar Al-Amin El-Kanemi, ya ce duk mai rai Allah ya kaddara ya mutu.
Uban Masarautar ya yabawa Gwamna Mai Mala Buni bisa wannan karimcin tare da addu’ar Allah ya jikan marigayin.
Takaitaccen bukin gabatar da taron wanda ya gudana a fadar mai martaba Sarkin Damaturu, ya samu halartar mai bawa gwamna shawara na musamman kan harkokin tsaro, Brig. Janar Dahiru Abdul-Salam (Rtd), Kwamandan Bataliya ta 233, Laftanar Kanal G. Abdul da sauran su.
A wani labarin kumaAn Kama Wasu Mutum Biyu Masu Yiwa Mutane Musayar Katin ATM A Suleja
Marigayin ya rasu ya bar matar sa mai ciki da ‘ya’ya hudu da kuma mahaifiyar sa daya.
Wannan lamari na bakin ciki ya haifar da martani a shafukan sada zumunta inda mazauna Damaturu ke kira da a gudanar da bincike mai kyau da kuma biyan diyya ga dangin mamacin.
Mazauna yankin sun danganta hatsarin da tukin ganganci da sojoji suka yi.