Daliban Kwalejin Gwamnatin Tarayya (FCG) Kwali, dake Abuja, an kwashe su daga dakunan kwanan su, sakamakon wani hari da aka kai a wata unguwa da ke kusa da su.
Da safiyar Litinin ne iyayen suka garzaya makarantar domin kwashe ‘ya’yansu daga kwalejin hadaka da ke kauyen Sheda, kan babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa da safiyar ranar Litinin din nan ne wasu iyaye suka ke kwalejin inda suka dinga kwashe ‘ya’yansu.
Wata mahaifiya mai suna Misis Babep Peace ta bayyana cewa ta zo ne daga Legas domin ta kwashe ‘ya’yanta biyu bayan da ta samu kira cewa hukumar kwalejin ta umurci iyaye da su kwashe yayansu.
Ta ce ta samu kiran ne da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Lahadi, lamarin da ta ce ya sa ta hau motar dare daga Legas, zuwa Abuja.
Wani jami’in kwalejin, wanda mamba ne na kungiyar iyayen yara (PTA), ya shaida cewa hukumar ta umurci iyaye da su gaggauta kwashe ‘ya’yansu saboda harin da ‘yan bindiga suka kai kauyen Sheda.
Kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, DSP Adeh Josephine, bata mayar da martani ga sakon da aka aike mata ba game da lamarin.
An sha yin garkuwa da jama’a daga makarantun kasar nan da mayakan Boko Haram da ‘yan bindiga ke yi.