An yi jadawalin Kungiyoyin takwas da suka rage a gasar cin kofin FA, domin buga matakin daf da na kusa da na karshe. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
An yi jadawalin na wasan kusa da na karshe ne bayan wasannin na ranar Laraba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sakamakon zabe: Yanzu aka fara gwabza faɗa – Martanin Dino Melaye Kan cewa dole a kori Tinubu
Manchester United wadda ta yi waje da West Ham da ci 3-1, za ta karbi bakuncin Fulham.
Abokan hamayyarsu Manchester City za ta karbi bakuncin Burnley a Etihad, yayin da Brighton za ta kara da Grimsby.
Ga dai cikakken jadawalin na FA a wasan daf da na kusa da karshe:
Man City vs Burnley
Man Utd vs Fulham
Brighton vs Grimsby
Sheffield Utd vs Blackburn
A wani labarin kuma, Dan takarar Sanatan PDP a Ogun ya yi fatali da sakamakon zabe
Dan takarar kujerar Sanata na jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) a jihar Ogun ta tsakiya, Cif Olumide Aderinokun ya yi watsi da sakamakon zaben majalisar da aka gudanar a ranar Asabar saboda abin da ya kira aringizon kuri’u da kuma wasu bambance-bambancen zabe.
Cif Aderinokun, wanda aka bayyana na biyu a zaben Sanata a bayan dan takarar jam’iyyar APC, Afolabi Salisu, ya ce akwai rumfunan zabe sama da 100 a Ogun ta Tsakiya da ba su kada kuri’a ba.