Arsenal Ta Taba Neman Maddison Amma Leicester Take Yarda Ya Bar Kungiyar
Leicester Ta Koma Gasar Yan Dagaji Ta Kasar Ingila
Tottenham Na Shiryr Shiryen Tunkarar Gasar Badi
Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Leicester City James Maddison ya koma kungiyar Tottenham Hotspur Dake buga gasar Firimiya Lig ta kasar Ingila
Maddison ya rattaba hannu akan yarjejeniyar shekaru 4 a kungiyar ta birnin London inda zai tsaya har shekarar 2027
Leicester City wadda ta lashe kofin Firimiya Lig a shekarar 2016-2017 sun koma gasar rukunin yan dagaji na Championship bayan rashin tabuka abin azo agani a kakar bana
Maddison Wanda ya bugawa kasarsa ta Ingila wasanni 3 ya koma Leicester City daga kungiyar Norwich City a shekarar 2018
KARANTA NANSauyin Yanayi: Mata Sun Dasa Shuka 5,000 A Makarantun Kaduna
Ya samu nasarar zurara kwallaye 55 da kuma taimakawa a jefa 41 ciki har da 10 da ya jefa a kakar bana,ya kuma taimakawa Leicester lashe Kofin Kalubale na FA Cup a shekarar 2021
Ya buga musu wasanni 203 tsawon shekaru 5 da ya shafe a King Power Stadium kafin ya yanke shawarar barin kungiyar bayan da suka kasa samun damar buga gasar Firimiya a badi
Tottenham Hotspur na neman kara karfin tawagarsu domin tunkarar kakar badi,zuwa yanzu sun dauko sabbin yan wasa 3 da suka Hada da Gugliemo Vicario wanda suka dauko daga Empoli
Sai kuma Dejan Kulusevski da ya zama Dan wasan din din din bayan kammala zamn aron da yakeyi daga Juventus dake buga gasar Serie A
Sabon Koci Ange Postecoglou na fatan kyaftin din kungiyar Harry Kane ya cigaba da taka leda duk da tayin fam miliyan 70 da Bayern Munich tayi akansa
DUBA WANNAN
Arsenal Ta Tura Tayin Fam Miliyan 105 Akan Rice
Arsenal Ta Tura Tayin Fam miliyan 105 akan dan wasan tsakiya kuma kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta West Ham United Declan Rice A Kokarin da suke na ganin sun kawo shi Emirates Stadium
Bayan kasa lashe kofin Firimiya Lig na bana da Arsenal tayi tana fatan tunkarar kakar badi da wasu sabbin yan wasa domin gwada sa’arta,inda zuwa yanzu da dauki Kai Harvertz daga Chelsea