Jami’a ta rage ma Ɗalibai kuɗaɗen Makaranta Saboda halin matsi da ake ciki
Jami’ar Jihar Legas a Najeriya ta rage kuɗin Makaranta ga Ɗaliban da ke karatu a Jami’ar.
Hakan ya biyo bayan wata ganawa da Shugabannin Jami’ar karkashin Jagorancin Shugaban Jami’ar Folasade Ogunsola suka yi da tawagar Shugabannin dalibai a ranar Alhamis.
Tawagar Ɗaliban sun samu Jagorancin Shugaban Kungiyar ɗaliban Najeriya ta ƙasa wato NANS Usman Barambu
Taron dai wani ɓangare ne na ƙoƙarin shawo kan tsadar kuɗaɗen Makaranta da ke damun Ɗalibai a wannan lokacin.
KARANTA WANNAN LABARIN:Zamu Tabbatar Zabukan Da Za’a Yi A Jahohin Imo,Bayelsa Da Kogi Sun Tafi Lami Lafiya-Yan Sanda
Jami’ar Adejoke Alaga Ibrahim da ke Legas ta sanar da rage kuɗaɗen da suka wajabta akan ɗalibai kamar kudade Makarantar, da kuɗaɗen morar kayayyakin Makaranta da na kammala karatu da sauran su.
An sake duba kuɗaɗen da suka wajaba ga sabbin daliban da za su fara karatun digiri inda ake rage kuɗin daga Naira 126,325 zuwa Naira 116,325 ga kwasa-kwasan da ba su da alaƙa da Lab ko Situdiyo, sai kuma kwasa-kwasai masu alaƙa da Lab ko Situdiyo inda aka rage masu kuɗin daga Naira 176,325 zuwa N166,325.
Haka kuma an sake duba kuɗaɗen da suka wajaba ga Ɗaliban da ke cikin karatu a kwasa-kwasan da ba su da alaƙa da Lab ko Situdiyo daga Nairan100,750 zuwa N80,750, sai kwasa-kwasai masu alaƙa da Lab ko Situdiyo inda Ɗaliban za su biya Naira 120,250 maimakon Naira 140,250, yayin da kuma ɗaliban likitanci da na sashen nazarin haɗa magunguna za su biya Naira 170,250 maimakon 190,250.
Tun bayan cire tallafin Man fetur da Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu yayi a ranar da aka rantsar da shi, Jami’o’i da dama suka bayyana ƙara kuɗaɗen Makarantar, lamarin da ya jefa dalibai da dama musamman ƴaƴan Talakawa cikin fargabar makomar karatun su.
A wani labarin kuma:Jami’ar Jihar Chicago ta fitar da sanarwa kan bayanan karatun Tinubu
Jami’ar Jihar Chicago ta fitar da sanarwa kan bayanan karatun Tinubu
Jami’ar jihar Chicago CSU ta tabbatar da cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya halarci jami’ar.