An sako wasu daliban jami’ar Obafemi Awolowo University, OAU, Ile-Ife, wadanda jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) suka kama kwanan nan.
Sakin nasu ya biyo bayan wata zanga-zangar da daliban makarantar suka yi, inda suka mamaye ofishin hukumar yaki da cin hanci da rashawa da ke Ibadan a jihar Oyo.
DAILY POST ta tattaro cewa jami’an EFCC sun cafke daliban da yawansu ya haura 70 a garin Ile-Ife na jihar Osun a wani samame da suka kai ranar Talata.
Karanta nanZan Daga Darajar Matasan Nijeriya A Idon Duniya–Ministar Matasa
Sai dai kuma dan majalisar dokokin jihar Osun mai wakiltar mazabar Ife ta tsakiya, Abiola Awoyeye, ya ce 58 daga cikin daliban da aka kama sun samu ‘yanci.
Ya kara da cewa, ana ci gaba da tattaunawa domin sakin sauran 11 da suka rage.
Zan iya tabbatar da cewa an saki 58 daga cikin mutane 69 da aka kama, tare da tattaunawa kan sauran 11,” in ji shi a kan X.
Ina so in gode wa Gwamna Ademola Adeleke da Babban Lauyan Gwamnati, Barr Wole Bada, bisa ga wannan bajinta da suka yi.
Jami’in hulda da jama’a na jami’ar Obafemi Awolowo dake Ile-Ife a jihar Osun, Abiodun Olarewaju, ya bayyana cewa an sako dalibai 58 daga cikin 69 na makarantar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta kama a baya.
Olarewaju, ya kuma bayyana cewa saura 11 na da kararrakin da za su amsa a gaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, ya bayyana cewa an sako daliban ne bayan wani taro da mahukuntan hukumar suka yi da hukumar EFCC a Ibadan.
A wani labarin KumaMiyetti Allah Ta Sha Alwashin Fitar Da Bata Gari A Cikinsu
Da yake zantawa da manema labarai a Ile Ife kakakin jami’ar, Olarewaju, ya ce mahukuntan hukumar za su yi taro da hukumar EFCC.
Sai dai ya ci gaba da cewa jami’ar ba za ta hana hukumar yaki da cin hanci da rashawa yin aikin ta ba.
Hukumar ta EFCC, a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Facebook da aka tantance bayan sa’o’i, ta tabbatar da cewa ta kama mutane 69 da ake zargi a Ile-Ife. Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta lissafa sunayen wadanda ake zargin amma ta yi shiru dangane da zamansu dalibai.