Hedkwatar tsaro ta sanar da cewa, Rundunar Operation Hadin Kai ta ceto ‘yan sanda 20 da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a wani hari da suka kai wa sashen ‘yan sanda da ke Buni Yadi na jihar Yobe.
Mukaddashin daraktan harkokin yada labarai na rundunar Birgediya Janar Benard Onyeuko, yayin da yake yiwa manema labarai karin haske kan ayyukan soji da ke gudana a cikin makonni biyun da suka gabata.
A cewarsa, a cikin lokacin da ake Kai famamen ga maboyar Yan tada kayar bayan, an kashe jimillar ‘yan ta’adda 62 tare da kama 28.