Wasu jami’an soji da suka yi ritaya a ranar Litinin din nan, sun bijirewa ruwan sama da aka yi a safiyar ranar Litinin domin gudanar da zanga-zangar kashi na uku a shedikwatar ma’aikatar tsaro da ke Abuja.
Masu zanga-zangar dai sun koka kan rashin biyansu alawus din tsaro da dai sauransu.
Masu zanga-zangar da suka hada da wasu ‘yan uwan ma’aikatan da suka rasu sun tare hanyar shiga ma’aikatar da ke gidan Ship House da ke kan titin Olusegun Obasanjo a babban birnin tarayya.
Tsofaffin sojojin da ke karkashin kungiyar Ma’aikatan Sojin Najeriya da suka yi ritaya da kuma gamayyar tsaffin sojojin da abun ya shafa sun zargi Ministan Tsaro, Manjo janaral Bashir Magashi (Mai Ritaya), na rashin kulawa da halin da suke ciki.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Da yake yiwa manema labarai jawabi yayin zanga-zangar, kakakin gamayyar CVV, Abiodun Durowaiye-Herberts, ya sha alwashin cewa ba za su bar kofar shiga ma’aikatar ba har sai an biya musu bukatunsu.
Ya ce tuni suka shirya yin barcin dare idan lamarin ya tabbata.
KARANTA KUMA: Sojoji Da Yan Sanda Sun Dakatar Zanga-zangar Dalibai
“Muna nan tare da matan mu da ‘ya’yanmu, da kuma matan da suka rasa mazajensu na ma’aikatan soja da tsofaffin da suka mutu a wajen aiki, wadanda wasunsu suka mutu a fada da ‘yan ta’addan Boko Haram. Za mu kwana a nan har sai Ministan Tsaro, Magashi ya amsa bukatunmu,” inji shi.
A nasa bangaren, Sakataren RMNAF na kasa, Roy Okhidievbie, wanda ya bayyana cewa zanga-zangar na neman a biya su alawus alawus na tsaro da suke bin gwamnatin tarayya .
Ya zargi Ministan da kin biyan alawus din duk da amincewar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi.
“Mun yi ganawa da Ministan Tsaro, Magashi, amma bisa ga dukkan alamu ya kasance mai taurin kai, son zuciya, kuma ba ya cikin damuwa game da korafe-korafen jami’an soja da suka yi ritaya, domin bai taba biyan ko nuna sha’awa ko damuwa wajen biyan wadannan alawus-alawus din ba, musamman ma alawus-alawus na jami’an tsaro”
“Abin sha’awa shine, gwamnatin shugaba Buhari ta amince da biyan wannan alawus, amma Magashi ya ki biyan kudin,” in ji Okhidievbie.
Anna Nanven, wacce ‘yan ta’addar Boko Haram suka kashe mijinta, Kofur, a lokacin da suka kai hari a barikin sojoji a Jihar Borno, a shekarar 2015, ta shaida wa wakilinmu cewa ta samu alawus guda daya ne kawai tun bayan rasuwar mijinta.
Har ila yau, daya daga cikin ‘yan uwan ma’aikacin da ya rasu, Misis Nanven ta ce, “miji na matashi ne, Kofur da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kashe a wani hari da suka kai a barikin da yake aiki.
“Yanzu ina zaune da iyayensa, kuma na haifa masa ‘ya’ya biyar, mata uku da maza biyu har ya rasu. Yaran ‘yan shekara 22, 20, 18, 15, da shekara bakwai, kuma manyan biyu, ‘yan mata, da ba su kammala makarantar Sakandare ba za su iya biyan kudin shiga jami’a ba saboda ba zan iya biyan kudin makarantarsu ba.
“Ina rokon Shugaban kasa, Ministan Tsaro, da ‘yan Najeriya su kawo mana agaji. Ni da ’ya’yana biyar muna fama da talauci saboda ba zan iya samun damar fara kasuwanci ba, kuma ba ni da aikin yi.”
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, ta ruwaito cewa sojojin da suka yi ritaya a watan Janairun wannan shekara sun kira ga ma’aikatun kudi da tsaro, da kuma majalisar dokokin kasar domin amsa bukatunsu.
Da aka tuntubi mai magana da yawun Ministan Mohammed Abdulkadir, ya umurci wakilinmu ya tuntubi babban sakataren ma’aikatar Ibrahim Kana.
Sai dai har yanzu ba a amsa kiraye-kirayen da aka yi wa wayar salular Mista Kana ba, kuma har yanzu bai amsa sakon da aka aike masa ba har lokacin da ake hada wannan rahoto.
A wani labarin kuma: Malaman Kwalejoji Sun Fara Yajin Aikin Da Ba A Taba Ganin Irinsa Ba
Dubban malamai da sauran ma’aikata ne za su fara yajin aikin daga yau litinin a wata takaddama kan albashi.
Kimanin mambobin Jami’o’i 4,000 (UCU) a kwalejoji 31 a Ingila za su dauki tsawon kwanaki 10 na yajin aikin a makonni masu zuwa.