Wani matashi ɗan Jahar Bauchi wanda ya shirya yin tattaki daga Bauchin Yakubun zuwa Kano domin yin tozali da shahararriyar ‘yan fim ɗin Hausar nan da aka fi sani da Aisha Humaira.
Matashin wanda ya bayyana cewa shi yana matuƙar son ganin jarumar a zahiri hakan ne yasa ya shirya yin tattakin nasa.
Sai dai tun kafin tafiyar tasa tayi nisa, jami’an tsaro suka kai gare shi suka kuma tsare shi tare da hana shi yin tattakin ido huɗun da ya ɗauri aniyar yi zuwa Kanon Dabo.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani Matashi Ya Roki Tsohuwar Budurwarshi Da Wasu Zafafa Kalmomi Masu Sosa Zuciya Kan Ta Dawo Cikin Rayuwarsa Su Cigaba da Soyayya. Sai dai kalaman sun sa Jama’a na kallon kamar ya samu taɓuwar kwakwalwa.
Jami’an sun umarce shi da ya yi gaggawar komawa gida cikin iyalansa
Jaridar Katagun Dailypost ce ta wallafa wannan labarin, wanda a cikin ƙanƙanin lokaci da wallafa shi, ya karaɗe kafafen sada zumunta da dama.
Wasu waɗanda suka bibiyi wannan labarin sun bayyana ‘ayoyinsu daban daban akan wannan labarin kamar haka:
@Aliyu Musa Bursali yace: Sunyi daidai
@Munkaila Abdullahi Headboy ya ce: Wllhi sunyi daidai.Tsabar son zuciya da rashin mafaɗi kana ji za’ayi sallar Azahar kana zaune sai daga baya wataƙila kayi ko kayi wata kabar wata ko kuma kaƙi yi ma, ba sadaka ba ƙyauta. Wai ka tashi ka luluko uwar tafiya daga wani gari zuwa wani gari wanda ko mota bata zuwa akan lokaci kayi ta tafiya a kasa wai dan kaga wani ko wata ba shirmen banza darashin tinani irin wannan da son zuciya kawai. Allah ka shiryar da mu hanya madaidaiciya
@ Usman Yusuf ya ce: Wlhy dama sun zane shi . Bazaiyi tattaki zuwa wajen mutanen kirki ba sai yan nanaye.. Wai bashada mafadi ne
@Ahmad Abubakar: Ya kamata arika haɗa musu da bulala duk Wanda aka kama.