Jami’an tsaro a Abuja sun kama wani ma’aikacin cibiyar rigakafin cutar COVID-19 da ke ba da katin rigakafin jabu ga wasu matafiya na kasashen waje.
Shugaban hulda da jama’a na hukumar kula da lafiya matakin farko ta kasa (NPHCDA), Mal .Mohammad Ohitoto ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Litinin din nan.
Wanda ake zargin, Dauda Abu-Huraira, ya kasance kafin a kama shi yana kula da na’urar daukar bayanai a wurin allurar COVID-19 a babban asibitin Wuse, da ke Abuja.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, An kama Abu-Huraira yana karbar kudade daga abokan huldarsa yana basu katin karya ba tare da an bi tsarin rigakafin ba.
“Babban Daraktan Hukumar Kula da Lafiya matakin farko ta kasa, Dakta Faisal Shuaib, ya yi gargadin cewa akwai tsayuwa a kan yadda za a kama duk wadanda ke da hannu wajen bayar da katinan rigakafin COVID-19 na bogi a ko’ina a Najeriya tare da gurfanar da su a gaban kotu.” Sanarwar ta ce.
A cewarsa, Shu’aib ya yabawa jami’an tsaro a kasar kan yadda suka taka rawa wajen cafke wanda ake zargin.
Shugaban hukumar NPHCDA ya kuma yabawa jami’an kiwon lafiya na tashar jiragen ruwa bisa hadin kan da suke yi a irin wannan kokarin.
Ohitot ya ce a baya an kama wasu ‘yan masu laifin da aikata laifin kuma tuni suna fuskantar sakamakon abin da suka aikata.
Ya roki jama’a da su daina karbar katunan jabu ba tare da sun bi tsarin rigakafin ba, don amfanin kansu.