Jami’an yan sanda a jihar Abia sun kwace iko da sakatariyar jam’iyyar PDP a jihar, a safiyar yau Alhamis.
Kazalika jami’an yan sandan sun kuma dakatar da duk wata zirga-zirga ta mutane a harabar Sakatariyar da kuma wajen ta.
To sai dai ko da wasu daga cikin masu ruwa da tsaki suka bukaci sanin dalilin hakan, yan sandan sun bayyana musu cewa umarni suka karba daga sama cewa su aiwatar da hakan.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar ta sanar da dage lokacin gudanar da zaben fidda gwani da ta tsara gudanarwa tun da fari.
Baya ga haka, ana ci gaba da samun rikicin cikin gida a jam’iyyar, inda ko da a jihar Kano a jihar Laraba sai dai hatsaniya ta faru tsakanin shugabannin jam’iyyar PDP na jihar da kuma na kasa.
Dangane da abun da ke faruwa a jihar Abia kuwa, Sakataren yada labaran jam’iyyar Fabian Nwankwo ya ce an baiwa ma’aikatan jam’iyyar hutun kwana ɗaya domin su huta a gida.