Hukumomin Jami’ar Tarayya da ke Gusau a Jihar Zamfara, sun umarci duk daliban da ke zaune a gundumar Damba ta Gusau da su koma Sabon Gida ko kuma su zauna a cikin babban birnin Gusau a babban birnin jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na makarantar Kwamared Umar Usman ya fitar, inda ya bayyana cewa daliban za su fi samun tsaro a garin Gusau ko kauyen Sabon Gida.
Karanta nanSojojin Nijeriya Sun Samu Nasarar Kwato Dalibai 4 Da Aka Sace A Jami’ar Gusau
Sanarwar ta ci gaba da cewa, Hukumomin jami’ar na son yin kira ga daliban da su koma Sabon Gida, wanda a yanzu ya ke da tsaro da jami’an tsaro dauke da makamai ko kuma su zauna a cikin babban birnin Gusau.
Wannan saboda sun fi fuskantar hare-haren ‘yan bindiga lokacin da suke zaune a bayan gari, musamman Damba.
Usman ya ci gaba da cewa, dakarun Operation Hadarin Daji da Metro Joint Patrol (Eagle Eye) sun yi nasarar ceto dukkan daliban makarantar hudu da aka yi garkuwa da su a ranar Asabar, 14 ga Oktoba, 2023, a Unguwar Sabon Garin Damba, Gusau.
A wani labarin kumaBa’a Fita Wata Ba:Barayi Sun Kuma Sace Dalibai Biyu Na Jami’ar Tarayya Dake Gusau
Biyu daga cikin daliban hudu da aka yi garkuwa da su sun tsere bayan an yi garkuwa da su yayin da sauran biyun kuma aka kubutar da su bayan da dakarun soji suka fatattaki ‘yan bindigar a wani mummunan artabu da ‘yan bindigar in ji shi.
Daga karshe ya kara jaddada wannan mataki da hukumar makarantar ta dauka inda ya bayyana cewar wannan umarni ne ba shawara ba.