Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ta bayyana dalilin ficewar tsohon shugabanta na kasa Farfesa Rufa’i Alkali da wasu mambobin jam’iyyar zuwa jam’iyyar All Progressives Congress, APC.
A wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Abdulsalam Abdulrasaq, ya fitar a ranar Larabar da ta gabata, ya ce Alkali, Farfesa Bem Angwe, Sanata Othman Hunkuyi da wasu da dama sun bar jam’iyyar ne saboda matsalar da suka samu da Kwankwaso.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa Alkali ya zama shugaban kungiyar na kasa a babban taron da ya tabbatar da kungiyar a ranar 30 ga Maris, 2022, amma ya bar jam’iyyar da mukaminsa a ranar 30 ga Maris, 2023, saboda zargin da ake yi masa na rashin jituwa tsakaninsa da Kwankwaso.
Karanta nanShugaban Kwadago Zai Shilla Kasar Waje Neman Magani Akan Dukan Da Ya Sha
A cewar sanarwar, Hunkuyi, mai rattaba hannu kan yarjejeniyar MOU wanda shi ma ya fice tun da dadewa, a nasa bangaren ya sha fama da Kwankwaso har ma a lokacin da yake rike da madafun ikon jam’iyyar a matsayin sakataren kungiyar na kasa.
Sanarwar ta ce, Hunkuyi ya koka da yadda ake yi wa jam’iyyar karan tsaye, da dorawa wasu mukamai, da kin sauraren wasu dalilai da dama a lokacin da yake hidimar jam’iyyar.
A wani labarin kumaKotu Ta Baiwa Gwamnatin Kano Sati Daya Ta Biya Biliyan 30 Ga Masu Shagunan Masallacin Idi
Jam’iyar mai alamar kayan gwari ta bayyana cewar daga cikin abubuwan da suka janyo ta rasa manya manyan ‘ya’yan jam’iyar akwai rashin jituwa tsakaninsu da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda shine ya yiwa jam’iyar takarar shugaban kasa.
A cewar Abdulrasaq, ficewar shugabannin jam’iyyar NNPP 26 ta afkawa jam’iyyar kamar tsawa a daidai lokacin da sabon shugabancin Dr Agbo Major ya kafa kwamiti na musamman da zai yi hulda da su.