By Abbas Yakubu Yaura
Jam’iyyar APC reshen jihar Legas ta bayyana rasuwar mataimakiyar shugabar majalisar dokokin jihar mace ta farko, Misis Adetoun Adediran a matsayin babban rashi.
Adediran, wacce kuma kafin rasuwar ta ta kasance tsohuwar shugabar mata ce a jam’iyyar APC ta Legas, ta rasu ne da sanyin safiyar Laraba bayan ta yi fama da gajeriya rashin lafiya.
Kakakin jam’iyyar APC na Legas, Mista Seye Oladejo, ya tabbatar da hakan a ranar Laraba lokacin da wakilinmu ya tuntube shi.
Ya ce, “Tsohuwar shugabar mata ce a Legas ta tsakiya, ’yar siyasa ce mai kwakkwarar manufa, jajirtacciyar shugabar al’ummarta wacce ta ba da gudunmawa sosai wajen ci gaban jam’iyyar da ci gaban jihar Legas. Za a yi kewar ta sosai.”
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Adediran ta kasance mataimakiyar kakakin majalisar wakilai mai wakiltan Surulere I tsakanin shekarar 1999 zuwa 2003.
An yi jana’izar ta a rumbun ajiyar Ikoyi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
A halin da ake ciki, kakakin majalisar dokokin jihar Legas, Mudashiru Obasa, ya bayyana marigayiyar a matsayin daya daga cikin fitattun ‘yan siyasa.
“A matsayinta na babbar jami’a a gidan, ta kasance mai himma wajen ganin an ji muryarta a tsakanin abokan aikinta wadanda galibin su maza ne,” in ji shi.
“Muna jimamin rasuwarta ne a daidai lokacin da ake son gogewarta da hikimarta don ci gaban jiharmu. Mun yi alhini saboda mutuwa ta kuma daya daga cikin fitattun ‘yan siyasarmu,” inji shi.