Jam’iyyar APC ta dakatar da babban taronta na kasa wanda aka shirya gudanarwa ranar 26 ga watan Fabrairu.
Jam’iyyar a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan Litinin 21 ga watan Fabrairu, 2022 kuma mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin riko da tsare-tsare na musamman (CECPC), Gwamna Mai Mala Buni da sakataren kwamitin, Sanata John Akpanudoedehe, tare da mika wa shugaban Hukumar Zabe Mai zaman kanta INEC.
Jam’iyyar ta Kuma ce za a gudanar da zabukan shiyyar ne a ranar 26 ga Maris, 2022 yayin da ake sa ran INEC za ta tura jami’anta don sanya ido kan aikin.