Jam’iyyar APC, a Cross River, ta sanar da dage ayyukan yakin neman zaben jihar da tun farko ta mayar dashi daga ranar 5 zuwa 10 ga Disamba, 2022 har sai baba ta gani.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren yada labaran jam’iyyar APC, Erasmus Ekpang, ranar Alhamis a Calabar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Majalisar Dattawa Ta Gaza Titsiye Shugabannin CBN Kan Kayyade Cire Kuɗi
Mista Ekpang ya ce za a sanar da wata sabuwar rana daidai da haka.
“Mun fahimci halin da ake ciki da rashin daidaito, wannan ya haifar da dimbin amintattun jam’iyyarmu da tun daga lokacin suka koma mazabar Sanatan Arewa a shirye-shiryen tunkarar zaben.
“Muna so mu nemi gafarar kowa da gaske kuma mu sanar da ku cewa wannan dage gangamin yakin neman zaben ya zama babu makawa saboda huldar kasa da kasa da ‘yan takarar jam’iyyarmu da masu ruwa da tsaki a Abuja.
“Muna so mu yi amfani da wannan kafar don yabawa tare da yin kira ga dukkan jam’iyya masu aminci cewa kowa zai samu abin alfahari a majalisar yakin neman zaben ko dai a matakin jiha, karamar hukuma ko kuma a matakin unguwanni.
“Manufarmu ita ce nasara ga jam’iyyar yayin da muke tabbatar wa duk jam’iyyar da ke da aminci cewa za ta kasance mai tsafta,” in ji Mista Ekpang.NAN
A wani labarin kuma, Hukumar INEC Ta Koka Da Karancin Masu Karbar Katunan Zabe A Jihar Borno
Kwamishinan Zabe na Jihar Borno na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Mohammed Magaji, ya koka da karancin masu karbar katin zabe tun lokacin da aka fara rabon kayayyakin a watan Satumbar bana.
Da yake jawabi a wani taron manema labarai a Maiduguri ranar Juma’a, REC ya bukaci duk wadanda suka yi rajista a yankin har yanzu ba su zo sun karbi katin zaben su na PVC ba dasu zo su karba cikin sauri.